Wasu mahara sun harbe Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Kamaru, Henry Kemende, har lahaira.
Bayan dirka wa dan majalisar harbi da maharan suka yi, sun kuma yi awon gaba da mai dakinsa.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Likitoci Ke ‘Jawo Asarar Rayuka’
- An yi garkuwa da ’yan kasuwa da ba a san adadinsu ba hanyar Kano
Mista Kemende dan siyasa ne daga jam’iyyar SDF kuma ya fito ne daga yankin Bamenda, inda ake amfani da harshen turancin Ingilishi.
Yankin da dan Majalisar ya fito shi ne cibiyar ’yan a-waren Ambazoniya da ke neman ballewa daga Kamaru, wandanda suke gwabza fada da dakarun gwamnatin kasar.
Tuni jami’an tsaro a kasar suka fara gudanar da bincike don gano ainihin wadanda suke da hannu a kisan Mataimakin Shugaban Majalisar.
Wasu dai na zargin Gwamnatin Shugaba Paul Biya da hannu a wannan kisa na daya daga cikin wakilan jama’a da ke kare manufofin al’ummar yankin da ke amfani da harshen Ingilishi.
Marigayi Henry Kemende wanda lauya ne, ya lashe kujerar dan majalisa a karkashin inuwar jam’iyyar SDF ne a zaben 2018 da aka gudanar a kasar.