✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An baza ’yan sanda 18,748 saboda zaben Kano

An gargadi iyaye da kar su bari a ribaci ’ya’yansu a matsayin karnukan siyasa.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce kimanin jami’an tsaro 18,748 ne aka baza a fadin jihar domin gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ranar 18 ga watan Maris.

Kwamishinan ’yan sanda, Mista Mamman Dauda ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a Kano.

Ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro za su samar da tsaro mai inganci a fadin runfunan zabe 11,222 da ke unguwanni 484 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Dauda ya ce tuni an bayar da cikakken umarnin gudanar da aiki ga kwamandojin kowanne yanki da jami’an ‘yan sanda na shiyya-shiyya domin aiwatar da su.

CP Dauda ya bayar da tabbacin cewa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a shirye suke don kare masu kada kuri’a da jami’an INEC a lokacin zabe da kuma bayan zabe.

“Ina mai bayar da tabbaci dari bisa dari ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda cewa za su iya gudanar da ayyukansu cikin walwala a ranar 18 ga Maris ba tare da wata barazana ga rayuka ko dukiyoyinsa ba,” inji shi.

Kwamishinan ’yan sandan, ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar sun kiyaye tanade-tanaden Dokar Zabe tare da tabbatar da cewa an gudanar da zabe na gaskiya da adalci a duk sassan jihar.

“Dole ne mu tashi tsaye mu mutunta hakkin ’yan kasa.

“Za mu hada kai da sauran takwarorinmu jami’an tsaro domin bai wa mazauna jihar damar zaben shugabannin da suke so.”

Ya kara da cewa, a shirye suke domin tunkarar duk wuraren da ake fargabar samun tashe-tashen hankula ko kuma barazanar tsaro.

Dauda ya kuma ce Babban Sufeton ‘Yan sandan ya bayar da umarnin baza ma’aikata na musamman guda 315 masu dauke da kayayyakin aiki na zamani domin tunkarar duk wata barazana ta tsaro a lokacin zabe da kuma bayan zabe.

“Ina mai tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su samar da yanayi mai kyau domin gudanar da zaben na ranar Asabar cikin lumana da kwanciyar hankali.

“Ba za mu lamunci duk wani lamari da zai iya kawo rudani kafin ko lokacin zabe ko bayan zabe ba; duk wani mutum ko kungiyar da aka samu da karya doka za su fuskanci fushin doka,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyaye da su sanya ido sosai a kan ’ya’yansu tare da gargadin kar su bari a yi amfani da ‘ya’yansu a matsayin ‘yan bangar siyasa.

(NAN)