A karshen makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta cimma matsaya da ’yan kungiyar Boko Haram kan batun sakin malaman Jami’ar Maiduguri uku da suka kame suka yi garkuwa da su a garin Magumeri, a hanyarsu ta zuwa binciken man fetur da kuma matan da ke raka wata gawar ’yar sanda, wadanda Boko Haram din suka kai masu hari a garin Damboa, suka kashe wadansu, suka yi garkuwa da wdanasu a farkon bara.
Shugaban kungiyar Malaman Jami’ar Maiduguri, Mista Dani Mamman ya nuna farin ciki kan sako malaman, inda ya ce “Babu shakka mun ji dadin sako malaman uku bisa matsayar da suka cimma da Gwamnatin Tarayya. Abin ya faranta mana rai kuma na ga kokarin gwamnati da kungiyar agaji ta Red Cross, wajen sako wadannan bayin Allah. Domin da gwamnati ba ta nuna kokari a kan abin da ICRC ta kulla ba, to da har yanzu ba a kai ga wannan matsayin ba.”
daya daga cikin ’yan uwan matan da aka sako, mai suna Kuchelli Williams ta bayyana farin ciki dangane da sakin matan, inda ta ce, “Wallahi na ji dadin sakinsu, domin akwAi ’yar uwata tun daga lokacin da aka ce an kame su, ba ma barci domin muna tunanin wane irin hali suke ciki, tun da yake ba mutuwa suka yi ba. Mun yi ta yi musu addu’ar Allah Ya kubutar da su, kuma ga shi kuma Allah Ya kawo lokacin, saboda haka mun gode da gwamnati ta amince ta shiga wannan yarjejeniya, sannan kuma mun gode wa kungiyar agaji ta Red Cross saboda sa hannunta , Allah Ya saka musu da alheri.”