Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta bankado shirin wasu bata-gari na tada hargitsi a zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a ranar Asabar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar ya gargadi wadanda suke shirin tada zaune tsaye a lokacin zaben da su sake tunani domin hakan na iya sanya su nadama.
- Yadda aka tsaurara tsaro a Majalisa kafin mika kasafin 2022
- Najeriya A Yau: ’Yan Siyasa Na ‘Buya’ Saboda IPOB A Anambra
CP Egbuka ya jadadda cewa dokar hana zirga-zirga a lokacin zabe musamman ga wadanda ba zaben za su yi ba, na nan daram.
Kwamishinan ya ce don tabbatar da samun tsaro yayin zaben, an aike da karin jami’an tsaro zuwa jihar don tabbatar da ganin an yi zaben lafiya an kuma tashi lafiya.
Ya ce, “Muna son sanar da cewa za mu yi kokarin kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa.
“Zan kuma yi amfani da wannan dama wajen kiran jam’iyyu da su ja hankalin mambobinsu, su kasance masu bin doka a yayin zaben da za a yi.
“Muna kuma kira da jama’a da su yi kokarin sanar da rundunarmu duk wani abu da suka yi zargi, ko wani abu na tashin hankali, ko kuma su sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa da su,” a cewarsa.