✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bankado malaman bogi 612 a Bayelsa

Kwamitin binciken ya bada shawarar daukar matakin da ya ce cikin gaggawa.

Kwamitin Gwamnatin Jihar Bayelsa kan bitar Matakan Kananan Hukumomi da Ma’aikatan Makarantun Firamare ya bankado ma’aikatan bogi 612 daga makarantun firamare da ke karbar albashi daga gwamnati jihar.

Kwamitin wanda mai ba da shawara ga Gwamna Douye Diri kan kudaden shiga, Timipre Seipulou yake jagoranta, ya gabatar da rahoton binciken ga gwamnatin jihar cewa daga cikin ma’aikatan firamare 7,207 a jihar, 612 na bogi ne.

  1. An kashe masu garkuwa a wurin karbar kudin fansa
  2. Mahara sun kashe mutum 9 a Filato

A watan Afrilu 2021, Gwamna Douye Diri ya kafa kwamiti mai mutum 33 don yin tantantace ma’aikata kananan hukumomi da makarantun firamaren jihar.

Da yake gabatar da rahoton ga Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya wakilci gwamnan, Seipulou, ya ce kwamitin ya duba jimlar kararraki 14,258 a kananan hukumomi daban-daban.

Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai ga Mataimakin Gwamna, Doubara Atasi, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ya nakalto kwamitin yana cewa ya yi bincike kan malaman firamare 7,207, ma’aikatan majalisar 5,893 da ma’aikatan lafiya 1,189.

Seipulou ya ce an gudanar da aikin tantance ma’aikata da albashin watan Maris na 2021 a matsayin samfuri wanda a dalilin hakan aka gano badakala.

Rahoton ya kara da cewa ma’aikata 573 ba sa cikin tsarin biyan albashi, yayin da aka samu sunan mutum 10 da ma’aikata 13 da suka yi ritaya da ke karbar albashin.

Da yake karbar rahoton, Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya yaba wa kwamitin kan yadda ya yi aiki tukuru.

Ya yi alkawarin isar da rahoton ga Gwamna Douye Diri tare da yin aiki kafada da kafada da dukkan hukumomin da abin ya shafa wajen aiwatar da abin da ya dace tare da aiwatar da shawarwarin kwamitin.