✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bankado asirin mai rainon da ta sace yaro

A Jihar Kurosriba, dubun wata mata mai aikin raino a wani gida da ke unguwar Satellite a birnin Kalaba ya cika.Matar mai suna Cobenant Bassey…

A Jihar Kurosriba, dubun wata mata mai aikin raino a wani gida da ke unguwar Satellite a birnin Kalaba ya cika.
Matar mai suna Cobenant Bassey ta sace yaron da take raino ta yi garkuwa da shi. Asirinta ya tonu ne bayan da jami’an tsaro suka tsananta bincike.
Uwar yaron mai suna Uche Robinson ta shaida wa Aminiya cewa mai rainon ta sace danta mai suna Dabid ne tare da wasu kadarorin gidan masu tsadar gaske, ta kuma arce da su.
John Eluu, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Kurosriba ya shaida wa Aminiya cewa a garin Fatakwal Jihar Ribas ne aka danko ta yayin da take kokarin sayar da yaron.
Mahaifin yaron mai suna Ekpedeme Robinson ya shaida wa wakilinmu cewa: “Na tafi makaranta dauko yarana tagwaye, koda na dawo gida na iske babu Dabid babu kuma motsin mai rainon, shi ya sa na bazama ofishin ’yan sanda da ke kan titin airport na sanar masu.”
Yanzu haka wadda ake zargi na tsare a hannun ’yan sanda kuma da zarar sun gama bincikenta za su gabatar da ita gaban kotu.