✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An banka wa barayin waya wuta a Delta

Barayi biyu aka kama kuma nan taka aka banka musu wuta.

Fusatattun jama’ar unguwa sun banka wa wasu barayi biyu wuta bayan da aka kama su sun yi wa wata mata fashin wayar salula a yankin Karamar Hukumar Warri ta Kudu da ke Jihar Delta.

Bayanan da Aminiya ta kalato sun nuna wannan al’amari ya auku ne a karshen makon da ya gabata, lamarin da ya fusata mazauna yankin.

Majiyarmu ta ce, “Barayi biyu aka kama kuma nan taka aka banka musu wuta, sai dai daya ya tsere da wuta a jikinsa.

“Wadan ya rasa ransa sunansa Lucky, sau da dama ana yi masa gargadin ya daina sata amma ya ki ji, shi ya sa da aka kama shi yana sata aka kashe shi.

“Daya da ya tsere da wuta a jikinsa, ba mu sani ba ko ya mutu ko kuma yana raye. Mun dai sani ya ji mummunar rauni saboda dukan da ya sha a hannun jama’a.”

Majiyar ta kara da cewa, “Kafin zuwan ’yan sanda wurin an riga an banka wa baarayin wuta.”

Da aka nemi jin ta bakin hukuma, Mai Magana da Yawun ’Yan Sandan Yankin (PPRO), ya ce, “Babu wanda ya kai wa ‘yan sanda rahoton hakan.”