Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce ta ankarar da Hukumar ’Yan sandan Duniya (INTERPOL) kan ta kama dan Majalisar Dattawa Sanata Dino Melaye da wadansu mutum shida.
A shekaranjiya Laraba ce aka tsara Sanata Dino Melaye da wadansu mutum shida za su gurfana a gaban wata kotu da ke Lakwaja fadar Jihar Kogi bisa tuhumarsu da hannun a wasu ayyukkan kisa da fashi da makami da garkuwa da mutane, amma sai ba su bayyana ba. Tuni Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Kpotun Idris, ya sauke Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kogi, Mista Ali Janga daga kan mukaminsa dalilin takaddamar.
Wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya, Jimoh Moshood ya aike wa manema labarai ta ce, an sauke Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kogi ne saboda guduwar mutum shida da aka tsare da su kan wannan batu.
Sanarwar ta ce an tsare wadansu ’yan sanda 13 da alhakin kula da mutane ke hannunsu kuma ana bincike a kansu game da rawar da suka taka kan guduwar mutanen.
Sufeto Janar din ya kuma umarci Kwamishinan ’Yan sanda, Esa Sunday Ogbu ya wuce Jihar Kogi ya kama aiki a matsayin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar. Ibrahim Idris ya kuma tura ayarin kwararu masu bincike a karkashin Abba Kyari zuwa jihar domin zakulo wadanda suka tseren kuma tuni suka isa garin Lakwaja domin fara aiki.
Rundunar ’Yan sandan ta ce mutum shidan da suka tsare tun farko sun bayar da shaidar cewa Sanata Dino Melaye yana goyon bayan ’yan fashi da ’yan bindiga.
Sai dai a hirar da ya yi BBC a baya-baya nan Sanata Melaye ya musanta zargin, inda ya ce Rundunar ’Yan sandan karya take yi don ba a taba gayyatarsa zuwa kotu ba, sai a kafafen watsa labarai ya ji labari. “Batun da aka ce wai Sufeto Janar na ’Yan sandan ya ce in je kotu ranar 20 ga wata, to ai ni a wannan rana ma ba na nan, ina Ghana tare da wadansu sanatoci ’yan uwana kan wani taro na harkar mai. Don haka babu wanda ya taba ba ni wata gayyata daga kotu, ko a wannan karon ma da suka ce ana nemana ranar 28 ga wata har yanzu ba wanda ya kawo takarda daga kotu cewa ana nemana,” inji shi.
Sanata Melaye ya kuma ce a yanzu haka rayuwarsa tana furkantar barazana ta yadda ba zai iya zuwa garin Lakwaja ba, babban birnin jiharsa ta asali, saboda “sau biyu ana nemi a kashe ni a can,” inji shi.
A zaman Majalisar Dattawa na shekaranjiya Laraba, Sanata Melaye ya bukaci ’yan sanda su nemo wadanda ake zarginsa tare da su, inda ya ce, lauyoyinsa sun riga sun hallara a gaban kotun tun misalin karfe 9 na safe a ranar, kuma an kira shari’ar amma mai gabatar da kara ya gaza gabatar da biyu daga cikin wadanda ake tuhuma. “Maimakon su gabatar da wadanda ake zargin sai suka nemi a bayar da umarnin kama ni, amma alkalin ya ki amincewa da bukatarsu, saboda ya san ba a kawo min sammaci ba, kuma na tura lauyoyina zuwa kotun. Kuma manyan wadanda ake zargi babu su a kotun,” inji shi.
Ya bukaci Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya kawo wadanda ake zargin gaban kotu cikin awa 48, in kuma ya gaza zai kai shi kara kan tayar masa da hankali.