Gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola, ya bawa bata garin da suka saci kayan abinci daga rumbun gwamnati da na sauran mutane sa’o’i 72 da su dawo da su ko su fuskanci hukunci.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin da yake ganawa da manema labarai a jihar jim kadan bayan rangadin ganin irin barnar da aka yi a wasu sassa dake jihar.
Oyetola ya ce, “Abubuwan da idanuna suka gane min yau ba komai bane face fashi da makami, saboda har injinan da ake aiki da su duk an kwashe”.
“Wannan abun Allah-wadai ne, saboda wannan babbar sata ce tare da fashi”.
“Dan haka zan iya cewa wannan ba zanga-zangar #EndSARS bace face fashi da satar kayan mutane da aka yi a ko ina”.
“A matsayinmu na gwamnati muna da hanyoyin da zamu bi domin hukunta wanda suka aikata hakan tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya”, cewar gwamnan jihar Oyetola.
Gwamnan yace duk wanda yasan ya saci wani nau’in abu ya tabbatar ya mika shi ga hukuma, shugabannin kananan hukumomi ko masu saratun gargajiya mafi kusa da shi.
Ya kara da cewa duk wanda suka aikata hakan to gwamnatin jihar zata yafe musu, wanda kuwa suka aikata sabanin hakan zasu fuskanci tsattsauran hukunci.
Barnar da bata garin suka aikata ta hanyar satar kayan tallafin rage radadin annobar COVID19 da ma fasa rumbunan mutane wanda ba mallakin gwamnatin jihar ba, ya sanya gwamnatin sake sanya dokar hana fita a ranar asabar din da ta gabata.