✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Yadda aka raba wa marayu 1,100 kayan sallah a Kano

Wata gidauniya ta raba wa marayu 1,100 kayan sallah kyauta a Jihar Kano.

Wata gidauniya ta raba wa marayu 1,100 kayan sallah kyauta a Jihar Kano.

Marayun da suka samu gudunmawar kayan sallar a ranar Laraba sun fito ne daga Kananan Hukuomin Garko da Wudil na Jihar.

Gidauniyar Muhammad Ali-Wudil ta ce ta raba wa marayun kayan ne domin sanya musu farin ciki a lokacin Karamar Sallah.

Darakan gidauniyar, Alhaji Baffa Alhaji ya ce yin hakan zai faranta musu rai su ji cewa ana kaunar su kamar yaran da iyayensu suke raye.

“Sun rasa iyayensu, saboda haka muka ga ya dace mu taimaka musu ta yadda su ma za su samu farin ciki.

“Ya kamata mawadata da ’yan siyasa su yi koyi wurin taimaka wa mabukata da marayu domin sanya musu farin ciki, sannan yin hakan akwai lada mai yawa.

“Tufafi na daga cikin muhimman bukatun dan Adam, shi ya sa muke ba su, saboda su ma idan sallah ta zo su fito cikin ado,” inji shi.

A cewarsa, baya ga tallafin kayan abinci da kudade, gidauniyar ta raba tufafi ga matan aure 300, limamai 52 da matasa kusan 1,000 a yankin a cikin watan Ramadan.

A nashi jawabin, wanda ya kafa gidauniyar, Alhaji Yusuf Lajawa ya bukaci wadanda suka samu da su yi amfani da yakan ta hanyar da ta dace kuma su taimaka da addu’ar samun zaman lafiya da aminci.