✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba hammata iska tsakanin Doguwa da Garo a Kano

Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC ta jihar Kano biyo bayan rashin fahimtar da ta shiga tsakanin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai,…

Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC ta jihar Kano biyo bayan rashin fahimtar da ta shiga tsakanin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da Mataimakin dan takarar Gwamna na APC a jihar, Murtala Sule Garo.

Rikicin na zuwa ne kimanin kwana uku bayan da dan takarar Shugaban Kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kammala taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar.

Masu fashin baki na ganin sabon rikicin da ya kunno kan zai iya yin tasiri ga tafiyar Tinubu a jihar Kano.

Aminiya ta kalato cewa, rikicin ya faro ne a ranar Litinin da daddare a gidan Mataimakin Gwamnan Jihar, kuma dan takarar Gwamna na APC, Nasir Yusuf Gawuna, yayin da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ke tattaunawa.

Ko a ‘yan watannin da suka gabata, jam’iyyar APC ta Kano ta yi fama da rikicin cikin gida bayan da tsohon Gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau da wasu jiga-jigai suka ware kansu saboda abin da suka kira da rashin adalci.

Da yake ta tabattar da faruwar lamarin a ranar Talata, Alhassan Doguwa ya ce ba a gayyace shi zuwa wurin taron a gidan Gawuna ba.

Ya ce ya tafi gidan ne don ganawa da shugaban jam’iyya na jihar, Abdullahi Abbas.

Ya kara da cewa, ko da ya isa gidan ya tarar da irin mutanen da taron ya kunsa, cikin ‘raha’ ya nemi jin abin da ya sa ba a gayyace shi taron ba a matsayinsa na dan Majalisar Tarayya.

A nan ne aka ce Garo ya amsa da ai ba komai ne sai an gayyace shi ba, amsar da aka ce ba ta yi wa Doguwa dadi ba wanda hakan ya haifar da ‘yar hatsaniya a tsakani.

Sai dai kungiyar GGDP da ke rajin tallata manufofin takarar Gawuna da Garo a matsayin Gwamna da Mataimaki a jihar Kano ta yi Allah-wadai da abin da Doguwa ya yi wa Murtala Sule Garo.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Litinin an sami hatsaniya inda Doguwa ya jefi Murtala Garo da kofin shayi har ya yi masa rauni.

Shugaban kungiyar wanda shi ne Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa, Aminu Jijitau da mataimakinsa Honorabil Aminu Dahiru wanda kuma shi ne Hadimi bangaren daukar hoto na Gwamna su ne suka bayyana hakan cikin wata sanarwa da suka sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce abin da Doguwa ya yi rashin girmama ne ga jam’iyyar APC ne da jagororinta musamman Gwamna Dokta Abdullahii Umar Ganduje don haka suna kira ga APC da Gwamna Ganduje da ya binciki abin da faru kuma a hukunta Alhassan Doguwa saboda abin kaico da ya yi wa jagoranmu”