Kungiyar nan mai rajin kawo daidaito kan tafiyar da ayyukan gwamnati (SERAP) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki zargin batan dabo da wasu kudade da yawansu ya kai Naira miliyan 300 suka yi.
Kungiyar ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya umarci ministan shari’a, Abubakar Malami, da hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da su binciki zargin cikin kwanaki 14.
A cewar kungiyar, kudaden da wani rahoton bin diddigi na ofishin babban akanta na Najeriya ya fitar kan hada-hadar kudade na shekara ta 2017 ya yi zargin an bi da su ta hanyar da ba ta dace ba.
- Za a hana gwamnoni taba kudaden kananan hukumomi
- Yajin aiki: Kungiyar ASUP ta baiwa gwamnati wa’adin kwanaki 21
“Muna bukatar ka dauki matakin da muka ba da shawara cikin kwanaki 14 daga fitar da wannan sanarwa; gaza yin hakan zai tilasta SERAP ta dauki mataki na shari’a da zai sa dole a yi hakan”, inji SERAP.
Wasikar mai dauke da kwanan wata 4 ga watan Yuli wadda kuma ke dauke da sa hannun mataimakin daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare, ta ce rahoton ya fito da yadda aka yi wa-ka-ci-ka-tashi da makudan kudaden ba tare da yin bayani kan yadda aka kashe su ba.
SERAP ta ce binciko wadanda ke da hannu a cikin badakalar tare da hukunta su zai taka rawa matuka wajen tabbatar da ikirarin da gwamnati mai ci ke yi na yaki da cin hanci da rashawa.
Ta kuma ce matakin zai tabbatar da gaskiyar ma’aikatu da hukumonin gwamnati musamman kan yadda suke kashe kudadensu.
“Duk wani yunkuri na kin binciken tare da hukunta masu laifin zai ci karo da tanade-tanaden dokokin kasa musamman ta fuskar yaki da karbar rasahawa da kuma kundin tsarin mulkin kasa”, in ji SERAP.