✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ba da umarnin cafko wadanda suka kona caji ofis a Imo

Bata-gari sun kuma kona kotun Majistaren yankin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo ta ba da umarnin kamo bata-garin da suka cinna wa ofishin ’yan sanda na Atta da ke Karamar Hukumar Njaba ta Jihar wuta a ranar Asabar.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin Rundunar, SP Bala Elkana, ya fitar cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Abutu Yaro, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

“Mun samu kiran agajin gaggawa cewar wasu bata-gari sun cinna wa Kotun Majistaren Attah wuta.

“Sun kuma kone wani gini da jama’ar yankin suka yi da nufin mayar da shi ofishin ’yan sanda.

“Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Abutu Yaro, ya ba da umarnin gudanar da bincike tare da kamo wadanda suka aikata laifin,” cewar sanarwar.

Tuni dai jami’an ’yan sandan jihar suka bazama don kamo tare da gurfanar da wadanda suka kona ofishin ’yan sandan a jihar.