Kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Gyadi-gyadi a Jihar Kano ta ba da belin alkalan nan da kuma ma’aikatan kotun Musulinci da ake tuhuma da bacewar kudi sama da Naira miliyan 500 na wasu marayu.
A tuhumar ta farko ana zargin mutane 15 da yin sama da fadi da Naira miliyan 96, ta biyu kuma ana zargin wasu mutum biyar ne kan bacewar Naira miliyan 408.
Bayan dogon nazari, alkalin kotun Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti, ya bayar da belin mutanen da ake zargi tare da gindaya musu sharuda kafin a sake su.
Sharadin belin tuhuma ta farko sun hada da kawo mutane biyu, na farko zai ajiye Naira dubu 200, na biyu kuma zai ajiye takardun gidansa ko fili da darajarsa ta kai Naira miliyan 10.
Sharudan belin tuhuma ta biyu kuwa su ne kowanne zai gabatar da mutane biyu tare da yin takardar rantsuwa da idan wanda ya tsayawa ya gudu zai biya Naira miliyan 5, sannan za su ajiye Naira miliyan 10.
Na biyu sai sun samo wanda yake da gida ko fili da darajarsa ta kai Naira miliyan 200 a Jihar Kano.
A karshe alkalin ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Fabarairu 2023.