✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ɗauki tubabbun ’yan daba 50 aikin dan sanda a Kano

Suna cikin mutum 222 da suka tuna kuma ake debe su aikim

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta dauki tubabbun ’yan daba 50 aikin dan sanda a Jihar.

Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar, Mohammed Usaini Gumel ne ya tabbatar da hakan yayin bikin yaye mutanen bayan sun shafe wata biyu suna daukar horo a matsayin ‘Constabulary’.

A cikin wata sanarwar da Kakakin rundunar a Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce tubabbun mutanen suna cikin guda 222 din da suka ajiye makamansu ne sannan suka bayar da kansu domin yin aiki a matsayin ’yan sanda a Jihar.

Daga nan sai ya bukace su da su nuna kwarewa da ɗa’a da kuka jajircewa sannan su yi amfani da aikin nasu wajen kare yankunansu.

Sanarwar ta kuma ce, “Idan za a iya tunawa, kimanin wata uku da suka wuce rundunarmu ta gayyaci wasu tatattun ’yan daba domin tattaunawa.

“A sakamakon haka, mun karbi takardun ’yan daba 222 sannan muka mika wa Gwamna yayin wasa kwallon kafar sada zumunta tsakanin ’yan sanda da su a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, domin a samar musu abin da zai canza musu rayuwa,” in ji sanarwar.