Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC ) ta kone jabun magunguna na kimanin Naira miliyan 985 a garin Kalibawa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano.
Shugaban Hukumar NAFDAC ta Kasa, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan da cewa za su ci gaba da zage dantse wajen yakin da suke yi da jabun magunguna da kayayyakin abinci a fadin kasar nan.
- Sarkin Kaltungo ya koya jama’arsa dabarun noman rogo na zamani
- Kasuwar Karu da ke Abuja ta yi gobara
Misis Adeyeye wacce ta sami wakilcin shugabar hukumar mai kula da shiyyar Arewa Maso Yamma, Misis Josephine Dayilim ta ƙara da cewa hana jabun magunguna yawo a tsakanin al’umma ita ce kaɗai hanyar da za ta sa ’yan ƙasar nan su kasance masu lafiya da bunkasar arziki.
A cewarta kayayyakin da NAFDAC ta kone sun hada da jabun magunguna da kayayyakin da lokacin amfaninsu ya kare kamar su abinci da kayan shafe-shafe da sauransu.
Ta ce an yi an hakan ne bayan hukumar ta ce tantance kayayyakin ta hanyar kwace su daga masu sayarwa da kuma wadanda mutane suka kawo wa hukumar bisa radin kansu.
A jawabinsa, Shugaban NAFDAC reshen Kano, Alhaji Kassim Ibrahim ya bayyana cewa babbar nasararsu ita ce yadda suka yi kokarin tashin masu sayar da magunguna daga Kasuwar Sabon Gari zuwa tsararriyar Kasuwar Magani da ke Dangwaro a Jihar Kano.
Ya kuma ce idan har suka dakile jabun magunguna a Kano kamar sun dakile matsalar ne a Najeriya gaba daya, la’akari da jihar ce cibiyar kasuwanci a kasar.
“Kasancewar Kano Cibiyar Kasuwanci ce za mu iya cewa kaso 90 cikin dari na magunguna da ke yawo a Arewacin Najeriya daga Kano suke.
“Saboda haka idan har aka yi nasarar dakile jabun magunguna da sauran kayayyaki to kamar mun dakile abin ne a Arewacin Najeriya da ma kasashen da ke makwabtaka da mu gaba daya.
Da yake jawabi wakilin Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Abba Adamu Takai cewa ya yi gwamnati ba za ta saurarawa duk wani mutum da ta kama yana shigowa ko kuma yana siyar da jabun magunguna a jihar ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, hukumomin da ke da ruwa da tsaki daban-daban ne suka halarci taron kona jabun magungunan da suka hada da Hukumar Kula da Magunguna ta Kasa (PCN) da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) da Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki (SON) da Hukumar Kula da Hakkin Masu Sayen kayayyaki (CPC), da Hukumar Kwastom da ta EFCC da Kungiyar Masu Sayar da Magani ta (NAPPMED) da sauransu.