Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe.
Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan kasa da shekaru biyar sama da 38,000 a fadin jihar.
- Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida
- Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya
Gwamnan ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba yayin da ya kaddamar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin fadada harkokin kiwon lafiya, musamman ga marasa galihu.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin jawabinsa a wajen babban taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Damaturu, wanda ya samu halartar sarakunan gargajiya da malaman addini, abokan hulda, ma’aikatan lafiya da manyan jami’an hukumar gudanarwa a bangaren samar da kiwon lafiya a matakin farko da kuma kungiyoyin farar hula.
Gwamna Buni ya bayyana manufarsa ta samar da lafiya mai rahusa a matsayin ginshikin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma.
Ya amince da goyon bayan gwamnatin tarayya da abokan hulda da suka hada da Gidauniyar Bill and Melinda Gates, Aliko Dangote Foundation, UNICEF, da WHO da dai sauransu.
Gwamnan ya jaddada kudirin jihar na samar da kiwon lafiya, inda ya ba da misali da kafa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 142, samar da kayan aiki da magunguna, da daukar kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sama da 2,000 a fadin Jihar.
Ya bayyana irin nasarorin da jihar ta samu ciki har da fitowar ta a matsayin zakara ta shekarar 2024 a bangaren samar da kiwon lafiya a matakin farko a fadin kasar nan ta Champion leadership for Primary Health Care PHC 2024.
Ya kuma yi tsokaci kan kafa Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Jihar Yobe (YSCHMA) da Hukumar Kula da Magunguna ta Jihar Yobe (YODMA) don magance kuɗaɗen kula da lafiya da samar da magunguna.
Kazalika, ya bukaci sarakunan gargajiya da su ba da goyon baya tare da bayar da gudunmawa wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a yankunansu.
Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsaki da su lura da batutuwan da aka tattauna a taron tare da magance kura-kuran da ake da su a yankunansu da kuma wuraren gudanar da ayyukansu domin kara inganta harkar kiwon lafiya a matakin farko a Jihar.