Gwamnatin Amurka ta sanar da shirinta na inganta karfin Intanet a nahiyar Afirka zuwa kashi 80 ciki 100 nan da shekarar 2030.
Amurka za ta inganta ƙarfin samun shiga yanar gizo daga kaso 40 cikin 100 da ake da shi yanzu a nahiyar.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwar da Mataimakiyar Shugabar Amurka, Kamala Harris ta yi a ranar Juma’a.
Sanarwar da ta yi na zuwa ne bayan shekara guda da ziyarar da ta kai nahiyar Afirka, a daidai lokacin da suka zanta da Shugaban Kenya, William Ruto a birnin Washington.
Wannan na daga cikin manufofin Amurkar na karfafa hulɗar tattalin arziki da nahiyar Afirka, nahiyar da hankali ya karkata kanta a matsayin wacce makomar ci gaba na duniya ya dogara da ita.
Bankin bunkasa kasashen Afirka da ma wasu ƙungiyoyi sun ƙara himma wajen inganta fannin sadarwar zamani, inda za a fara da samar da Intanet mai ƙarfi ga manoma a ƙasashen Kenya da Tanzaniya da ma Najeriya a tashin farko kafin abin ya kai ga sauran ƙasashen na nahiyar.
A bara ce dai Kammala Harris ta ziyarci kasashen Ghana, Tanzaniya da Zambiya, inda ta bayyana ƙudirin Amurka na inganta harkokin intanet da ci gaban fasahar zamani a nahiyyar.