’Yan tawayen Houthi na Yemen sun yi barazanar cewa Amurka za ta gamu da fushinsu muddin ta kai wa Iran hari a rikicin da ya ɓarke tsakaninta da Isra’ila.
’Yan tawayen sun ce za su kai wa jiragen ruwan Amurka hare-hare a Tekun Bahar Rum, idan har Washington ta yi kuskuren shiga yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar wa Iran, duk kuwa da yarjejeniya tsagaita wuta da aka cimma a baya-bayan nan.
A cikin wani faifan bidiyo, kakakin ’yan tawayen Houthi Yahya Saree ya bayyana cewa, muddin Amurka ta kai wa Iran hari ko kuma ta shiga cikin wannan rikici, mayankansu za su ƙaddamar da farmaki kan muradun Amurkar da suka haɗa da jiragen yaƙi da kuma jiragen dakon kaya da ke zirga-zirga a Tekun Bahar Rum.
Wannan barazana ta ’yan tawayen Houthi na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donad Trump ya saka wa’adin makonni biyu domin yanke shawara a game da yiwuwar shiga rikicin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran inda aka shiga mako na biyu suna yi wa juna ruwan bama-bamai.
Sai dai kuma tuni Amurkan ta ƙaddamar da hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran kamar yadda Shugaba Donald Trump ya bayyana a daren Asabar wayewar gari Lahadi.
A wata sanarwar da Trump ya fitar a jawabin da ya yi a talabijin yana iƙirarin sun tarwatsa cibiyar, ya ce “hare-haren na soji babbar nasara ce.”
Trump ya ce Amurka ta kai hare-haren ne a yankunan Natanz and Isfahan na cibiyar nukiliyar Fordo wurin da Iran ke aikin shirin bunƙasa makamashinta na Uranium da ke can ƙarƙashin ƙasa.
A cikin jawabin, Trump ya ce ko dai Iran ta nemi zaman lafiya ko kuma ta fuskanci mummunan bala’in fiye da wanda aka gani a kwanaki takwas da suka gabata.
“Amurka za ta sake kai wa Iran hari idan har ba ta nemi yin sulhu ba,” a cewar Trump.
Gwamnatin Iran ta tabbatar da hare-haren amma ta ce babu wani lahani da suka yi wa cibiyoyin nukiliyarta, sannan kuma ta musanta ikirarin cewa an tarwatsa cibiyoyin.
Hukumar makamashi ta Iran ta ce hare-haren na rashin hankali ne da suka saba wa dokokin duniya, kuma hukumar ta ce hare-haren ba za su hana Iran ci gaba da cimma muradin ta ba na samar da makamin nukiliya.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya la’anci hare-haren na Amurka yana mai cewa kasarsa za ta yi duk mai yiwuwa domin tana da hakkin kare ’yancinta.
Shi dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya taya Trump murna kan hare-haren, yana mai cewa “da karfin gaske da adalci na Amurka zai canza tarihi.”
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da hare-haren na Amurka, inda Antonio Guterres ya ce babbar bazarana ce ga zaman lafiyar duniya kuma mataki ne mai hatsari na kara rura wutar yaki, haka ma kasashe aminan Iran irinsu Cuba da Venezuela sun yi Allah-wadai da hare-haren.
Tun a ranar 13 ga watan Yuni ne Isra’ila ta ƙaddamar da hari kan Iran, tana mai cewa ta yi hakan ne domin kawar da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya, bayan Firaiminista Benjamin Netanyahu ya yi iƙirarin cewa Iran na dab da mallakar makamin.
A matsayin martani, Iran ta ƙaddamar da hare-haren ɗaruruwan makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa kan Isra’ila, inda ƙasashen biyu suka ci gaba da musayar wuta ta sama, tsawon sama da mako ɗaya.