✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka za ta daina ba Hukumar Lafiya ta Duniya kudi —Trump

Amurka za ta daina bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) kudi saboda gazawarta wajen gudanar da aikinta a yadda ta tunkari annobar coronavirus. Shugaba…

Amurka za ta daina bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) kudi saboda gazawarta wajen gudanar da aikinta a yadda ta tunkari annobar coronavirus.

Shugaba Donald Trump ne dai ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar White House yana mai cewa ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa hukumar kudaden da Amurka ta saba ba ta har sai an gudanar da bincike.

“Na ba da umarni ga jami’an gwamnatina su dakatar da samar da kudi yayin da ake nazari a kan rawar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta taka wajen mummunan sakaci da yin rufa-rufa game da barkewar annobar coronavirus”, inji Mista Trump.

Amurka ce dai kasar da ke bayar da tallafi mafi tsoka ga WHO, inda a bara ta samar da kusan Naira biliyan 15 ga hukumar.

Trump ya ce Amurka ta jima tana kyautata wa hukumar, amma yanzu ya kamata a diga ayar tambaya a kan wannan karimci da take yi.

“Da barkewar annobar COVID-19 a fadin duniya, mun damu matuka a kan ko ana amfani da wannan karimci na Amurka ta hanyar da ta dace”, inji shi.

Shi ma dai Donald Trump din ya sha suka a cikin gida a kan yadda ya tunkari annobar.

Kwanan baya hukumar ta WHO ta nuna takaici da yadda ta ce kasashen duniya sun yi shakulatin bangaro da gargadin da ta yi tana kira da su mayar da hankali wajen daukar matakan dakile cutar cikin hanzari.

Wasu manazarta dai na ganin wannan mataki ka iya jefa yakin da ake yi da cutar ta COVID-19 a fadin duniya cikin rudani.