Shugaban Amurka Donald Trump ya amince ya mika Gwamnati cikin lumana ga Shugaba Mai Jiran Gado, Joe Biden, bayan Majalisar Dokokin Kasar ta tabbatar da nasarar Biden a zaben Shugaban Kasa.
A safiyar Alhamis Majalisar ta tabbatar da Mista Joe Biden a matsayin Shugaban Kasa Mai Jiran gado, matakin da ke matsayin mahangurba ga ga Mista Trump, mai kalubalantar zaben, wanda magoya bayansa suki yi kutse a zauren Majalisar ranar Laraba domin tarwatsa majalisar.
An yanke wa karamar yarinya al’aura a Bauchi
Mista Trump ya ce matakin “ya kawo karshen mashahurin wa’adinsa na mulki a karo daya.”
“Duk da cewa ban amince da sakamakon zaben ba, da kuma kawar da ni, amma duk da haka za a samu mika gwamnati cikin kwanciyar hankali da tsari ranar 20 ga watan Janairu,” inji Shugaba Trump mai barin gado.
Said dai ya ce “Ina kan baka ta cewa za mu ci gaba da yunkurinmu na ganin ba a yi murdiya ba.
“Yayin da wannan lamari ya kawo karshe gagarumin wa’adin mulki na farko, a tarihin Shugabancin Amurka, shi ne kuma farkon yakinmu na sake daukaka martabar Amurka,” inji shi a yayin da yake magana game da hukuncin Majalisar da ya harzuwa magoya bayansa.
Kirgen zaben da aka yi ya ba wa Biden da Mataimakiyarsa Kamala Haris gagarumar nasara da fiye da maki 270 da ake bukata domin lashe zaben shugaban kasar.
Majalisar Wakilai da ta Dattawan kasar sun kuma yi watsi da bukatar soke kuri’in da Biden ya samu a jihohin Georgia da Pennsylvania.
’Yan Jama’iyyar Republicans sun kuma kalubalanci sakamakon jihohin Arizona, Nevada da Michigan inda Biden ke da rinjaye, sai dai kudurin nasu bai samu goyon baya ba.
Majalisar ta ci gaba da aikinta na tabbatar da nasarar Biden da Kamala Haris ne bayan tarzomar ranar Laraba a magoya bayan Trump suka yi a gininta ta Capitol.
Da farko boren ya kawo tsaiko na awanni ga zaman Majalisar na hadin gwiwa, kafin jami’an tsaro su fatattaki masu tarzomar aka kuma ci gaba da zaman da misalin karfe 8 na dare karkashin Mataimakin Shugaban Kasa, Mike Pence.