Gwamnatin Amurka ta sanar da janye tallafin Dala miliyan 442 da take ba wa Jamhuriyar Nijar a hukumance.
Amurka ta sanar da hakan bayan da ta ayyana kwace mulkin da sojojin kasar suka yi a watan Yuli a matsayin juyin mulki.
Wani babban jami’in Amurka ya ce, kasarsa ta “dauki matakin ne saboda a tsawon wata biyu da suka gabata mun bi duk hanyoyin da suka kamata domin dawo da halastacciyar gwamnati a Nijar amma abin ya gagara.”
Hakan na zuwa ne a ranar da rukuni na biyu na sojojin Faransa suka fice daga Nijar, tun bayan juyin mulkin da sojoji karkashin Janar Abdourahmane Tchiani suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.
Amurka da Faransa sun kafa sansanonin soji domin taimakawa wajen yakar ta’addanci a Nijar a zamanin Bazoum, wanda sojojin ke zargin sa da kasancewa dan amshin shatan Faransa.