Amurka ta cire kasar Sudan daga jerin kasashen masu taimaka wa ayyukan ta’addanci, shekara 27 bayan sanya sunan Sudan din a cikin jerin kasashe masu taimaka wa ’yan ta’adda.
Ofishin Jakadancin Amurkar a Khartoum, hedikwatar Sudan, ya ce Sakataren Harkokin Wajen Kasarsa ya sanya hannu a takardar cire Sudan daga cikin masu taimaka wa ta’addanci a duniya.
- Idan Sudan ta biya kudi zan cire ta daga jerin ‘yan ta’adda – Trump
- Sudan: An dage shari’ar juyin mulkin al-Bashir
Sanarwar ta ce umarnin wanke Sudan daga zargi zai fara aiki ne daga Litinin 14 ga Disamba, 2020.
A watan Oktoba, Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta cire Sudan daga jerin kasashen da ake zargi da taimaka wa ayyukan ta’addanci.
Sai dai a lokacin sabuwar gwamnatin ta ki amincewa da tayin saboda wasu bukatu da Amurka ta gabatar mata a kan hakan, duk da cewa hare-hare na hana masu zuba jari daga waje shiga kasarta.
Daga baya ta amince da biyan diyyar Dala miliyan 335 ga wadanda suka sha da kyar, da iyalan wadanda hare-haren da aka kai Ofisoshin Jakadancin Amurka a Kenya da Tanzania a shekarar 1998 suka hallaka.
Gwamnatin wucin gadin Sudan, wacce ta dare madafun iko bayan kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir a 2019, ta kuma amince da Isra’ila a matsayin kasa mai zaman kanta.