Shugaban Amurka, Joe Biden, ya bukaci ’yan kasarsa da ke zaune a Ukraine da su gaggauta ficewa, inda ya ce barazanar mamaya daga kasar Rasha na karuwa a kullum.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wutar rikici ke kara ruruwa tsakanin Amurka da Rasha, bisa zargin da ake yi wa Rashan na kokarin mamaye kasar ta Ukraine.
- ’Yan Bindiga Sun Dauke Mai Shayarwa da Danta a Zariya
- ’Yan fashi sun kashe ’yan sanda, sun wawushe kudi a motar daukar kudi
A cikin wani jawabi na musamman ta kafar yada labarai ta NBC, Shugaba Biden ya ce, “Ya kamata Amurkawa su gaggauta ficewa. Ba wai muna cewa suna fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda ba ne, sai don muna fuskantar kasar da daya ce daga cikin wadanda suka fi kowanne yawan sojoji.
“Yanayi ne na tsaka mai wuya, kuma kowanne lokaci al’amura na iya dada rincabewa,” inji shi.
Shugaba Biden ya kuma tabbatar da cewa babu wani dalili da zai sa ya tura dakarun Amurka zuwa Ukraine, ko da kuwa don ceto Amurkawan, idan ma Rasha ta mamaye kasar.
“Wannan yakin duniya ne. da zarar Amurkawa da mutanen Rasha sun fara harbin juna, to tabbas mun shiga wani mummunan yanayi ke nan,” inji shi.
Gargadin Shugaban dai na zuwa ne kwana daya bayan Sashen Harkokin Waje na kasar shi ma ya shawarci Amurkawan da su gaggauta ficewa daga Ukraine din, yayin da wadanda ke ciki kuma ya shawarcesu da su yi taka-tsantsan.