Gwamnatin Amurka ta ce ta amince ta sayar wa da Najeriya makaman yaki na Dala miliyan 997, kwatankwacin Naira biliyan 413.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Juma’a.
- Hare-hare 16 da ’yan bindiga suka kai cikin sati 2 a Arewa
- Ta kashe kanta saboda mijinta zai kara aure
Sanarwar ta ce makaman sun hada da jiragen yaki masu sakar angulu guda 12 da wasu makamai na harbawa guda 2,000 da kuma na’urori masu gani har hanji.
Hakan dai na zuwa ne bayan an shafe tsawon lokaci ana kwan-gaba-kwan-baya kan cinikin, inda Amurkan ta ki yarda ta sayar da makaman ga Najeriya saboda zargin take hakkin bil-Adama.
Amurka, a cewar sanarwar, za ta sayar wa Najeriya makaman ne don kasar ta bunkasa kokarinta na bunkasa tsaro.
Sanarwar ya ce, “Ma’aikatar Tsaron Amurka ta amince da bukatar sayar da makaman yakin sojoji ga Gwamnatin Najeriya jiragen yaki masu saukar angulu samfurin AH-1Z da sauran kayan aikinsuu, da kudinsu ya kai kusan Dala miliyan 997.
“Hukumar Kula da Kera Makamai ta Amurka ta amince da bukatar, kuma tuni ta mika sanarwar yin cinikin ga majalisa don ta amince da shi yau [Juma’a].
“Wannan cinikin da ake kokarin yi zai taimaka wa manufofin Amurka a kasashen ketare ta hanyar samar da tsaro ga muhimmiyar kasa a yankin Kudu da hamadar Sahara da ke Afirka,” inji sanarwar.