✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka da EU za su hana taba kadarorin Putin da Lavrov

Rasha ta ce haramcin na nuna gazawar kasashen Yamma

Amurka ta bi sahun Birtaniya da Tarayyar Turai (EU) wajen sanar da cewa za ta haramta taba kadarorin da Shugaba Vladimir Putin na Rasha da Ministan Harkokin Wajensa Sergey Lavrov suka mallaka.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa Ma’aikatar Kudin kasar ta Amrka ce ta sanar da daukar matakin jim kadan bayan EU ta ce ta amince da haramta taba kadarorin Putin da Lavrov a matsayin wani bangare na takunkumin da ta kakaba wa Rasha.

Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ma ya shaida wa shugabannin kungiyar tsaro ta NATO yayin wata tattaunawa da ya yi da su ta waya cewa kasarsa za ta kakaba takunkumi a kan Putin da Lavrov.

Tasirin haramcin

Sai dai kuma babu tabbas a kan tasirin da haramcin taba kadarorin zai yi a kan Putin da Lavrov, amma dai hakan hannunka mai sanda ne ga shugaban na Rasha cewa yana iya zama saniyar ware a duniya idan bai kawo karshen mamayar Ukraine ba.

Hakan kuma na nuna yadda kasashen Yamma suke daukar sababbin matakai a yunkurin tilasta wa Rasha ta kawo karshen mamayar.

Ministan Harkokin Wajen Austria, Alexander Schallenberg, ya ce matakin “shi ne irinsa na farko a tarihi da aka dauka a kan wata kasa da ta mallaki makamin nukiliya, kasar da take da wakilci a Kwamitin Sulhu [na Majalisar Dinkin Duniya], amma kuma ya nuna yadda kanmu yake a hade”.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya ambato hukumomin Rasha suna cewa wannan matakin ya fito da raunin kasashen na Yamma fili.

Sun kuma yi gargadin cewa kasashen na Yamma na daf da kaiwa magaryar tukewa.

‘An kusa kai mu iya wuya’

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta Rasha, Maria Zakharova, ta ce “mun kai wani mataki wanda daga shi za a fara kaiwa magaryar tukewa”.

Shugabannin EU ne dai suka amince da wannan takunkumi, irinsa na biyu a wannan makon a daidai lokacin da Rasha ta matsa kaimi wajen kai hari, yayin wani taron koli da suka yi cikin dare.

Takunkumin ya shafi bangarorin hada-hadar kudi da makamashi da sufuri na Rasha, ya kuma takaita damar da Rashawa suke da ita ta ajiyar makudan kudi a bankunan kasashen EU.

Ya kuma kara yawan daidaikun mutanen Rasha da aka haramta musu shiga kasashen EU aka kuma hana su taba kadarorinsu.