Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce kasar ba ta da allurar rigakafin cutar COVID-19 a lokacin da ya karbi mulki a watan Janairu, 2021.
Biden ya fadi haka ne yayin jawabi game da rigakafin COVID-19 da Amurka ta fara batun yi a kasarta a watan Disamba zamanin Donald Trump wanda Biden ya gada a Fadar White House.
- Ko sisi ba za mu biya diyya kan daliban Kagara ba –Gwamnatin Neja
- Buhari ya tura sojoji don kubutar da Daliban Kagara
“Abun da muke cewa shi ne wani abu ne daban a ce ana da rigakafin, wanda kuma ba mu da shi a lokacin da muka karbi mulki, amma kuma akwai mai yin allurar rigakafi.
“Ta yaya za ka isar da rigakafin jama’a” inji Biden ya zauren tattaunawar shugaban kasa da tashar talabijin ta CNN ta shirya ranar Talata.
Sai dai tohuwar Sakatariyar Yada Labarai ta Fadar White House, Kayleigh McEnany ta kira maganar Biden ”babbar karya,” domin Trump ne “wanda ya kawo allurar rigakafi mafi sauri ta wata sabuwar cuta tarihi.”