✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amunike ya haye da Tanzaniya gasar cin Kofin Afirka bayan shekara 39

Tsohon dan kwallon Najeriya Super Eagles, Emmanuel Amunike ya samu nasarar hayewa da kasar Tanzaniya zuwa gasar cin Kofin Afirka na bana wanda za a…

Tsohon dan kwallon Najeriya Super Eagles, Emmanuel Amunike ya samu nasarar hayewa da kasar Tanzaniya zuwa gasar cin Kofin Afirka na bana wanda za a yi a watan Yunin a karon bayan shekara 39.

Rabon da kasar ta halarci gasar cin Kofin Afirka tun a 1980.

Koci Amunike ya samu wannan nasara ce bayan Tanzaniya ta lallasa kasar Uganda da ci 3-0 a ranar Litinin da ta wuce wanda ya ba ta damar hayewa zuwa gasar da za ta gudana a kasar Masar..

Tanzaniya dai ta lallasa Uganda ne da ci 3-0 a filin wasanta na Dar es Salaam.  ’Yan kwallon Tanzaniya Simon Msuwa da Erasto Nyoni da kuma Aggrey Morris ne suka zura kwallayen da ya ba kasar tasu nasara.

A watan Agustan 2018 ne Emmanuel Amunike ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyu da kasar Tanzaniya don horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar.  Ga shi ya ba marada kunya inda ya haye da kasar zuwa gasar cin Kofin Afirka a karon farko cikin shekara 39.

Amunike yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da suka samu nasarar lashe Kofin Afirka a 1994 kuma yana daga cikin wadanda suka lashe lambar zinare a wasan kwallon kafa a gasar Olamfik da aka yi a Atlanta a 1996.

Ya horar da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya a matakin U-17 da U-21 da kuma U-23 a lokuta daban-daban kafin ya tafi Tanzaniya don horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar.