✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi kan kiwon lafiya daban-daban

kanwar mahaifiyata na da ciwon koda da ake yi wa wanki duk bayan kwana biyu. Shi ne muke tambaya haka za a ci gaba ke…

kanwar mahaifiyata na da ciwon koda da ake yi wa wanki duk bayan kwana biyu. Shi ne muke tambaya haka za a ci gaba ke nan har sai ta ji sauki ko kuwa ya za a yi?

Daga Ibrahim Abubakar

 

Amsa: Ai Alhaji Ibrahim in dai ka ji ana yi wa mutum wankin koda to fa kodar jikinsa duka biyun sun kasa yin aikinsu na fitar da ruwa da guba da wasu sinadarai da suka taru suka yi yawa a jiki. Domin kuwa ko da kodar kwaya daya na aiki, da wuya ma a zo wannan gaba. To sai dai idan wannan matsala ta kodar ta wucin gadi ce, kamar idan wasu abubuwa ne suka toshe koda biyun kamar tsakuwa ko kari ko tsuro, wanda ake tunani za a iya tiyata a cire, ko idan hawan jini ne ya kumbura ta, wanda ake ganin akwai maganin da zai sa ta farfado, to likita zai muku bayanin lokacin da yake hasashen za a daina wankin kodar, kamar idan an yi tiyatar ko an ba da magani kodar ta farfado. Wato ke nan ka ga  mai ciwon koda za a iya yin tiyata a cire matsala ko a sha magunguna su sa matsalar ta yi sauki, ko a rika taimaka mata wajen aikinta ta hanyar wanki na dialysis, ko ma a hada duka ukun. To wasu cutukan na koda idan aka yi musu haka ana sa ran su farfado. Idan ma akasin haka ne, wato ba a sa ran kodar za ta dawo aiki, duka dai shi ya kamata ya muku bayani. A wannan hali ne idan ba a sa ran koda ta farfado za a ce za a yi ta wankin koda ba kayyadajjen lokaci. Don haka a wannan hali, ko dai a ci gaba da wankin har abada ko kuma a yi wa mutum dashen wata sabuwar koda kwaya daya.

Dashen sabuwar koda shi ne magani na dindindin ga mai matacciyar koda, kuma in da hali ita ya kamata a nema a yi wa wanda duk aka ce kodarsa biyu sun mutu. Amma kafin a samu kodar da za ta dace da jikin maras lafiyar, dole a ci gaba da wankin kodar yadda aka tsara. A yanzu a kowane sashe na kasar nan, Gabas da Yamma Kudu da Arewa akwai manyan asibitoci da ake dashen koda.

 

Me ke sa jikin mutum ya kumbura, musamman fuska da kafafuwa?

Daga Maryam Maraba

 

Amsa: Ciwon koda, ko na hanta ko na zuciya ko ciwon borin jini mai tsanani, su ne a likitance ke sa kumburin jiki da fuska da kafa. Amma sai an duba mutum an dan yi aune-aune akan tantance ko wane ne daga cikinsu.

 

Me ke sa fatar ido ta dan taso ko ta dan kumbura idan an tashi daga barci?

Daga Aisha Aliyu

 

Amsa: Wannan ba wani kumburin rashin lafiya ba ne, alama ce ta cewa jiki har ma da fatar idon duk sun huta sosai. Amma idan fuskar ce gaba daya ke kumburi ai kin ga akwai matsala.

 

Idan har lemukan kara kuzari wato energy drinks na iya illa a likitance kamar yadda ka ce, me ya sa Hukumar tace abinci da magunguna ta NAFDAC ta amince da su?

Daga Mukhtar Ashiru

 

Amsa: Ai shi ya sa watakila fadakarwar irin wannan ta bakin masana kiwon lafiya take da amfani. Don wannan hukuma ta ba da amincewarta a sayar da abu ba zai zama ya inganta dari bisa dari ba. Ruwan barasa iri nawa hukumar ta amince da su? Amma hakan ai bai mayar da barasa amintaccen abin sha ba a likitance. Kuma ko su kansu hukumar za su tabbatar maka da haka, cewa shan ruwan barasa ko wane iri ne na lalata kwakwalwa da hanta.

 

Ni mai yawan so na ji jikina fes-fes ne, sai ta sa ma har nakan yi wanka da omo. Ko shin hakan zai iya jawo matsala?

Daga Muhammad Lawal, Bauchi

 

Amsa: A’a Malam Muhammadu ai hankali ma ba zai dauki wannan ba. Kamar mutum ne maimakon ya ci tuwo, sai ya ci ciyawa ko dusa. Ko masu aikin canzawa da sayar da bakin mai ai ba na jin da omo suke wanka. Kai wasu masu karfi a cikinsu ma in ka yi wankin tufafi da su za su iya tsaga maka fatar hannaye ballantana fatar jiki. Don haka ne ma wasu sukan sa safar roba a hannayen idan za su yi wanki don kada hakan ta faru.

 

Me ke sa zufa ne a wasu sassa na jikin mutum fiye da wasu sassa kamar hamata?

Daga Alhassan Ali Garba

 

Amsa: Bambancin kwayoyin halitta ne a wadannan wurare. Akwai kwayoyin halitta masu sarrafa ita zufar a wurare da dama akan fatarmu, amma kwayoyin halittun wasu sassan jiki sun fi na wasu sassan jikin girma da saurin sarrafawa da fitar da zufa. Duk inda mutum ya fiya fitar da zufa kamar wuraren da ka zayyana, nan ne inda kwayoyin fitar da zufa suka fi girma da yawa da aikin sarrafawa da fitar da zufar. Irin wadannan wurare ko ba yanayin zafi ba sukan fitar da zufa, sabanin wasu wuraren da sai ka shiga rana ko ka ji zafi ko ka yi aiki mai yawa. To da yake kuma iska ba ta ratsa wuraren sosai, nan da nan zufar za ta fara tsami. Shi ya sa ake son amfani da abubuwa irinsu hoda ko man roll-on don kamar da zufar.

 

Me ke kawo kuraje wadanda kan zama miki a cikin baki?

Daga Adamu Kainuwa da Mubarak dan Kurmi, Matazu

 

Amsa: Akwai dalilai da ba su wuce biyu zuwa uku ba masu kawo kurajen baki masu zama miki. Manyan daga ciki sune kwayoyin cuta musamman na fungus da na birus. Daga nan sai karancin wasu sinadarai na bitamin, ko bayan hucewar zazzabi, wanda shi ma yana da alaka da karancin bitamin din. Idan likita ya gani zai iya tantacewa ko na menene ya kuma ba da magunguna da shawarwari yadda za a yi a kiyaye aukuwarsu .

 

Mene ne ma’ana da bambancin wadannan kalmomi na jikin dan Adam ne; wato ‘hormone’ da ‘gland’?

Daga Reezan A., Wushishi

 

Amsa: ‘Hormone’ sinadari ne da wani sashen jiki ke fitarwa domin aika sakonni ko umarni daga wani sashen jiki zuwa wani. Shi kuma ‘gland’ shi ne gidan da ake sarrafa wadannan sinadarai. Misali sinadarin insulin, sinadarin ‘hormone’ ne da wani sashe na jiki da wasu kan kira nane-bango ko manne-bango (wato pancreas) yake samarwa don a aika shi sassan jiki ya ba da umarnin tsotse suga a jiki. To ka ga a nan sindarin insulin din shi ne ‘hormone’ shi kuma manne-bangon shi ne ‘gland’. Da fatan an fahimta.