✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi Da Suka Shafi Fata (2)

Likita, game da bayaninka na kayan shaye-shaye, shin da gaske ne ke nan ruwan zoborodo na maganin hawan jini?  Amsa: E, ganyen zoborodo wanda a…

Likita, game da bayaninka na kayan shaye-shaye, shin da gaske ne ke nan ruwan zoborodo na maganin hawan jini? 

Amsa: E, ganyen zoborodo wanda a kimiyyance ake kira Hibiscus Sabdariffa, a duniya baki daya an dade ana amfani da shi tun zamanin iyaye da kakanni a matsayin abin sha musamman a kasashen Indiya da na Larabawa da Malesiya da Sudan da Mali da nan gida Najeriya. Ana jika shi ganyen a yi abin sha a wasu wuraren a matsayin shayi a wasu kuma a matsayin lemo. A wancan zamanin an yi amfani da shi a matsayin maganin cushewar ciki. Duk tsawon wannan lokaci da ake amfani da shi a wadannan kasashe ba a taba ba da labarin yana sa wa jiki illa ba. Wannan ne ya sa masu bincike suka dukufa wajen bincikar sinadaran da ke cikinsa har suka gano akwai amfanuwa da dama a tare da shi.
Binciken masanan halittun itatuwa ne da dama, da na masu hada magunguna, ba ma na kasar nan kawai ba, har ma da na kasashen waje ya tabbatar da cewa idan mutum yana da hawan jini sa’annan ya samu ruwan zoborodo ko shayin zoborodo kofi guda yana sha kullum, to cikin sati biyu zuwa hudu za a fara ganin hawan jininsa yana sauka. Wato ba da mutum ya sha yau, gobe hawan jinin ke sauka ba, kamar yadda magungunan hawan jini ke aiki. Wasu masanan ma suka ce shan kofin ruwan zoborodo guda a kullum na tsawon sati hudu zai iya saukar da hawan jini daidai da yadda wani maganin hawan jini na captopril ke yi. Yadda suke irin wannan bincike a kimiyyance shi ne, a samu masu hawan jini da dama, rabi a dora su a kan ruwan soborodo, rabi kuma a ba su wancan magani. Bayan sati hudu suka auna hawan jininsu suka ga kowa nasa ya sauka.
Amma ya kamata ka gane ruwan zoborodo ba maganin hawan jini yake ba, rage hawan jini yake. Kai duk magungunan hawan jini ma rage shi suke ba su warkarwa, domin wasu idan aka ce magani, suna tunanin waraka. To ita matsalar hawan jini ba kayar cuta ba ce da za a ce idan ta mutu ciwon ya mutu ke nan, yanayi ne na mutum ke kawo hawan jini, ko dai gado, wanda dole ke nan yana cikin kwayoyin halittun gado, ko dai kiba, ko ciwon koda da sauransu. Ka ga ke nan sai an kawar da sababin kafin hawan jini ya tafi gaba daya. Mu yawanci abin da ke kawo mana hawan jini kiba ce, wadda idan da za mu rage ta da ta rabu da mu. To amma rage kibar kuma a tsaya haka tsawon shekaru ba a kara lafta wata ba, na da matukar wahala. Don haka mai hawan jini da ba a riga an dora a kan magani ba zai iya gwada wannan amma da sharadin zai rika zuwa ana auna shi a asibiti, idan soborodo bai yi ba, dole a canza.
Game da matsalolin fata, likita ina da kasumba ne da ke yawan fito min, idan na aske sai ya rika fitar da kuraje. Shin akwai yadda za a yi ya daina fitowa ko kuma ya daina fitar da wannan kuraje idan na aske shi?
Daga Abdullahi Isa, Jos
Amsa: Idan na fahimce ka, kai maimakon zubewar gashi, kai watakila mai yawan samun tsurowar gashi ne a jiki sosai har a kasumba. To ba kai kadai ba ne, wato ba wata matsala ba ce ta rashin lafiya ko wani aibu. Haka kai kuma yanayinka yake, saboda watakila ka gado yawan gashi. Masu wannan halitta za a ga suma kusan a ko’ina a kan fatarsu, musamman kirji, hannuwa, kafafuwa, hammata, mara da sauransu.
Kamar yadda in dai kana da rai da lafiya, farce ko kumba ke fito maka a duk bayan ’yan kwanaki, to kusan dole ne suma ma ta fito a wuraren da ta saba, sai dai ta wani ta fi ta wani, don haka a fara maganar kiyaye fitowar farce ma ko suma ka ga ba ta ma taso ba. Kamar ka ce kana son yadda za a yi ka daina bayan gida ne fa misali. Ka ga ko in dai da rai da lafiya ai ya zama dole. Don haka a likitance babu wani magani da za ka sha ko ka shafa da zai hana gashi fitowa. Ko ka samu ma, to illarsa gare ka za ta fi amfanin yawa.

Dabarar da ake wa kasumba idan an zo aski don kada ta yi kuraje ita ce:
1-Ka tabbata abin askin sabo ne ko tafasasshe. Ma’ana idan ba sabo ba ne sai ka tafasa don ka kashe kwayoyin cutar da ya nada.
2-Ka shafa man aski a fuska na tsawon minti biyu kafin ka yi askin don ya sa wurin taushi.
3-Kada ka rika dawo da abin askin wurin da ka riga ka aske, wato kada ka rika diddirzawa.
4-Idan ka gama ka samu ruwan magani na spirit ko maganin kurajen fuska ka shafa a inda ka yi askin.
5-Zaka lura kuma cewa sai fa ka aske sarai ne kuraje ke fitowa, wato sai ka tabo fata sa’annan kuraje za su fito. Idan mutum ya yi aski kasa-kasa, wato ya rage yawan sumar bai sude ta ba, kuma bai kai fata ba, ba shi ba wasu kuraje da za su fito.
Wai shin likita tsakanin manja da man gyada wanne ne ya fi kara lafiya ga jiki ne? Domin wasu sai ka ga suna miya da man ja, wasu kuma da na gyada.
Daga Amina, Kankiya
Amsa: A kimiyance man gyada ya fi manja amfani domin sinadaran maiko da ke cikinsa ba masu nauyi ba ne, wato ba masu sa wa magudanan jini da zuciya illa ba ne sosai. Shi man ja maikonsa yana da nauyi kuma magudanan jini ba su cika son maiko mai nauyi ba sosai. Sai dai shi man ja yana da sinadarin bitaman na rukunin A, mai kara lafiyar ido, wanda man gyada ba shi da shi. Dukkansu suna da sinadarin bitaman na rukunin E, mai gyara fata daidai-wa-daida. Don haka idan za a ba da shawara, kamata ya yi manya su fi sa man gyada a miya fiye da man ja, su kuma kananan yara a fi sa musu man ja a abinci fiye da man gyada.
Sauran man girki da sinadaransu ba su da nauyi sosai sue na man kade, man zaitun, man waken soya. Sauran masu nauyi ban da man ja su ne irinsu man kwakwa da man bota ta sa wa a burodi ko cake, da man kakide da na shanu.