✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: Barka da Sallah!

Barka da Sallah!A yau ga mu dauke da wasu daga cikin tambayoyinku da na tattaro daga wurare da dama.  Akwai wadanda suka aiko tambayoyi ta…

Barka da Sallah!
A yau ga mu dauke da wasu daga cikin tambayoyinku da na tattaro daga wurare da dama.  Akwai wadanda suka aiko tambayoyi ta hanyar lambar wayar dake wannan shafi, amma kasancewar katin SIM din ba a wayar salula yake ba (yana cikin Phantom Pad N9 ne, wata na’urar sarrafa bayanai mai kama da iPad), na samu hadari irin na cikin gida, inda na’urar ta fadi kasa, shafin gilashinta na gaba (screen) ya yi raga-raga.  Ko na kunna ba na iya ganin komai.  Kuma wannan hatsari ya faru ne kwanaki biyu kafin tattaro wadannan sakonni, wannan yasa ban samu kaiwa ga wadancan tambayoyi naku da kuka aiko ta katin SIM ba.  Wanda kuma, abin baki ciki, su ne suka yawa.  Don Allah a gafarce ni.  Ba wai shi ke nan ba, bayan sallah zan kai ofishin kamfanin da ya kera na’urar don a canza mini wannan gilashi, sai in tattaro su.  
Bayan haka, ina son jama’a su rika yawaita tambayoyi kan wasu fannonin ilimi da bayanansu ke gudana a wannan shafi, ba wai fannin kimiyya da fasahar sadarwa kadai ba.  Duk da cewa na san tasirin yaduwar na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani ne kan sa haka, kasancewar kowa na amfani da su kuma akan samu matsaloli yau da kullum.  
A karshe, ina yi mana addu’ar Allaha ya karbi ayyukanmu kyawawa da muka gudanar cikin wannan wata mai alfarma da yake mana bankwana, ya sa muna cikin ‘yantattun wannan wata, amin.  Ina yi mana murnar BARKA DA SALLAH da ke tafe nan da ‘yan sa’o’i in Allah ya so.
—————————————–
Assalamu Alaikum, da fatan Baban Sadik na cikin koshin lafiya.  Don Allah yaushe za a cigaba da fassara mana littafin “Why Astronomy”? – Faisal Muhammad
Wa alaikumus salaam Malam Faisal.  A gaskiya mun dakatar da batun fassara littafin a wannan shafi saboda wasu dalilai.  Amma akwai kokari na musamman don ci gaba da fassara shi, da kuma bugawa don yada shi cikin al’umma in Allah ya so.  Idan na gama tattaunawa da marubucin asalin littafin, wato Dokta Adnan Abdulhamid, in Allah ya yarda za a ci gaba da aikin a wannan tsari, ba a tsarin baya ba.  Ma’ana, idan batun bugawa ne, da zarar an buga zan sanar.  Akwai masu da dama suka tuntubeni kan wannan batu ba da jimawa ba, wasu ma sun bukaci in tura musu bangaren da na fara fassara wa wanda aka sa a shafin wannan jarida tamu mai albarka, na kuma tura musu.  Don haka da zarar na samu wani karin bayani da ba wannan ba, za ka ji ni ta wannan shafi ko ta dukkan shafukan da nake fadakar da masu karatun wannan shafi a duniya.  Da fatan ka gamsu
Assalamu Alaikum Baban Sadik, yaya azumi?  Ina fatan kana cikin koshin lafiya da kai da iyalanka?  Don Allah ina son ka bambanta mini tsakanin“Computer Laptop,” da “Computer Desktop” wajen mu’amala da keyboad, da mouse.  Sannan, wacce tafi saukin aiki? – Muhammad Auwal Koko danbaba
Wa alaikumus salaam Malam Muhammad, barka da warhaka.  Da fatan kaima kana cikin koshin lafiya.  Idan aka ce: “Laptop Computer” ana nufin kwamfutar tafi-da-gidanka ke nan, wacce za ka iya sanyawa a cikin jaka ka yi tafiya da ita, sannan idan a zaune kake kana iya dora ta a kan cinyarka kayi amfani da ita.  Babban abin da take samar shi ne saukin mu’amala a lokuta daban-daban.  Shi yasa take dauke da batir mai taskance makamashin lantarki na wasu sa’o’i, kuma sauran bangarorinta duk an takaita su, don baiwa mai ita samun rike ta, da daukanta, da tafiya da ita, da kuma mu’amala da ita ko a cikin jirgin sama yake, cikin sauki da gamsuwa.  
A dayan bangaren kuma, idan aka ce: “Desktop Computer” ana nufin kwamfuta ce wacce ke dauke da dukkan bangarorinta ko kamatsenta, daban-daban, wacce ba a iya mu’amala da wani bangarenta shi kadai kawai, dole sai da sauran bangarorin a wuri daya kuma a lokaci guda.  Galibi a saman tebur ake dora ta, shi yasa ake kiranta “Desptop” wato “Wadda ake dorawa a saman teburi.”  Sabanin kwamfuta nau’in tafi-da-gidanka (wato Laptop), ita “Desptop” galibin bangarorinta daban suke; sai an tashi mu’amala da ita ake jojjona mata su.  Kamar su allon shigar da bayanai (Keyboard), da Monita (Monitor), da uwar kwamfutar (System Unit), da beran kwamfuta (Mourse) da sauran komatse masu alaka da ita.
Tsarin mu’amala dangane da abin da ya shafi allon shigar da bayanai (Keyboard) da beran kwamfuta (Mouse) kamar yadda ka bukata, a fili yake.  Ita kwamfutar tafi-da-gidanka komai nata a wuri guda yake.  Duk da cewa za ka iya jona mata na’urar Beran kwamfuta don karin saukaka mu’amala, amma ko babu shi kana iya mu’amala da ita.  Amma a bangaren asalin kwamfuta kuwa, dole sai da Beran kwamfuta, sai in kwararre ne kai wajen iya mu’amala da kwamfuta.  Kowannensu na da saukin mu’amala, illa ya danganci kwarewarka ne.  Idan ka kware wajen iya amfani da kwamfuta kana iya samun gamsuwa wajen mu’amala da nau’in tafi-da-gidanka, wato “Laptop” ke nan, domin za ka fi jin dadinta sama da asalin kwamfuta, sai in kana da wasu ayyuka na musamman da kake son yi a kan wancan babbar.  Amma idan makoyi ne kai, zan bayar da shawarar ka lazimci nau’in “Desktop”, wato ta kan teburi kenan.  Ga makoyi, ta fi saukin mu’amala, kuma ta fi baka damar fahimtar hatta su kansu bangarorin kwamfutar, da aikin kowanne daga cikinsu.  Amma ita tafi-da-gidanka komai nata a matse yake, a hade yake, a cure yake.  Sai kwararre ke iya bambance su.  Sannan ko gyaran kwamfuta za ka koyi, dole sai da kwamfutar kan teburi za a fara koya maka, saboda galibin bangarorinta na bukatar karantarwa ta musamman, don su ma bukata na iya sa a nemi gyara su idan suka lalace.  Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa.  Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ina yi maka fatan alheri. Malamina tambaya akan yadda ake hada wayar tafi-da-gidanka da kwamfuta domin yin kira na bidiyo. Sannan wace waya ke iya wannan amfanin? – Aminu Umar Galadi
Wa alaikumus salam, Malam Aminu barka dai.  Ai ba na tunanin akwai wani tsari na sadarwa da kawai za ka iya don aiwatar da kiran bidiyo (bideo Call) a tsakanin wayar salula da kwamfuta.  Sai in kana nufin masu dauke da Intanet ne da kuma masarrafar da ake iya aiwatar da kiran da su.  Amma haka kawai, tsurar wayar salula da tsurar kwamfuta ba ka iya aiwatar da kira, dole sai da tsarin sadarwa na wayar salula (Mobile Network) da kuma yanayin sadarwa na Intanet da zai hada wadannan na’urori guda biyu da masarrafai ko manhajar da ke dauke a cikinsu.
A hakikanin gaskiya, da wayar salula da kwamfuta dukkansu tituna ne kawai.  Manhaja ko masarrafar (Applications) da ke dauke a cikinsu ne ke aiwatar da hakikanin abin da ake muradi na sadarwa.  Don haka, idan kana da wayar salula mai dauke manhajar kiran bidiyo (bideo Call App), kana iya kiran abokinka da ke kan shafinsa na Facebook ta hanyar manhajar “Facebook Chat” wato masarrafar hirar ga-ni-ga-ka da ke shafin Facebook.  Idan ka budo windon da ke dauke da sunan abokinka a wannan manhaja, ka duba sama daga bangaren dama maso tsakiya, za ka ga tambarin na’urar bidiyo sai ka matsa. Muddin yana da na’urar daukan hoto a kwamfutarsa (Webcam), nan take za a sanar da shi cewa: “Wane yana son hira da kai ta hanyar na’urar kira da bidiyo.”  Da zarar ya amince shi ke nan, sai ka fara ganin fuskarsa shi ma yana ganin naka, kuma hira ba matsala; iya gwargwadon karfin yanayin sadarwar intanet da ke dauke cikin na’urorin naku.  To, ka ga a nan, ka aiwatar da wannan kira na bidiyo ne tsakanin wayarka da kwamfutar abokinka, amma dole hakan bai yiwu ba sai ta dalilin samuwar manhajar kira na bidiyo (bideo Call App) da ke wayarka, da samuwar na’urar daukar hoto a kan kwamfutarsa, da kuma samuwar tsarin sadarwa na intanet a kan dukkan na’urorin naku gaba daya.
Bayan tsarin kiran bidiyo dake dauke a shafin Facebook, akwai masarrafai da yawa da aka gina masu iya gudanar da kira a tsarin bidiyo a kan wayoyin salula irin na zamani.  Akwai masarrafar Skype, wacce ta shahara a duniya, kuma da wannan masarrafa galibin tashoshin yada labarai na duniya na talabijin ke amfani don hira da jama’ar da ba za su iya riskuwa da su ba ta dadi sanadiyyar tazarar tafiya ko kurewar lokaci.  Akwai masarrafar Skype da ke kwamfuta, sannan akwai ta wayar salula.  Bayan Skype akwai masarrafar bibo da ke galibin wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Android a halin yanzu.  Ba wadannan kadai ba, akwai wasu da yawa da idan ka bincika “Play Store” (idan kana amfani da Android ne) ko “Store” (idan kana amfani da Windows Mobile ne) za ka same su; wasu kyauta ne, wasu kuma sai ka biya.  
Ba zan iya gaya maka sunayen wadannan wayoyi ba don suna da yawa.  Sai dai a duk sa’adda ka je sayen waya kana iya gaya musu cewa kana bukatar wacce ke iya aiwatar da kira a tsarin bidiyo ne, za su baka.  Domin sun yawaita sosai kuma farashinsu ya sha bamban.  Ina iya gaya maka wata ya zama kudinka ba zai iya mallaka ba, ko kuma za ka iya saya, amma ya zama tsarinta wajen kerawa da kamfanin da ya kera wayar bai yi maka ba.  Da fatan ka gamsu da wannan takaitaccen bayani.  
Assalamu alaikum Allah gafarta malam. Don Allah ayi mini bayanin matakan da zan bi don aiki da “Whatsapp” a kan kwamfuta. Allah ya kara ilmi mai albarka da takawa. – Abdulkadir Muhammad Bello
Wa alaikumus salaam Malam Abdulkadir, barka da warhaka. Wannan ai abu ne mai sauki.  Da farko sa’adda manhajar “Whatsapp” ta fara bayyana, babu wani tsari da za ka iya amfani da ita a kan wata na’ura idan ba wayar salula ba.  Amma daga baya, da masana harkar gina manhajar kwamfuta suka yi nazarinta, sai suka samar mata da “mazauni” da za ta iya gudanar da aiki a kan kwamfuta; ya Allah kwamfutar tafi-da-gidanka ce ko ta kan tebur.  Kamfanin da ya yi wannan kuwa shi ne kamfanin “Bluetstacks,” kuma sunan masarrafar da ya kirkira shi ne: “Bluestacks App Player.”
Wannan masarrafa dai ba don manhajar “Whatsapp” kadai aka gina ta ba.  A a.  Duk wata masarrafa da ka san ba a iya gudanar da ita a kan kwamfuta sai wayar salula, to kana iya saukar da ita a kan wannan masarrafa ta “Bluestacks App Player” don gundanar da ita, cikin sauki.  Wani abin sha’awa ma shi ne, wannan masarrafa kyauta ake bayar da ita, duk da cewa kana iya biyan kudin layi na tsawon shekara don samun karin damar amfani da masarrafar idan kana so.  Wannan masarrafa na amfani da manhajar “Play Store” ko “Google Store” ne, don saukarwa da kuma samun manhajoji, kamar yadda za ka iya a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android.  Kai, a takaice ma dai, tana bayar da damar iya amfani da masarrafan da aka gina su don babbar manhajar Android ne a kan kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Windows ko OS d na kamfanin Apple.
Don iya amfani da manhajar “Whatsapp” a kan kwamfutarka, sai ka je shafin Bluestacks dake: www.bluestacks.com ka saukar da manhajar zuwa kwamfutarka.  Idan ka je shafin, a kasa daga bangaren hagu za ka ci karo da tambarin “Download for Windows,” nan za ka shiga.  Idan ka gama saukar da masarrafar, sai ka loda wa kwamfutarka, wato “Install” ke nan.  Akwai matakai guda biyu da take bi; a farko masarrafar za ta loda kanta kan kwamfutarka.  Daga nan kuma za a ce maka: “ka dakata” don ta lodo wasu jakunkunan bayanai masu taimaka mata aiwatar da aikin cikin sauki.  Wadannan jakunkunan bayanai tana kiransu: “Library files.”  Hakan zai dan dauki lokaci, duk kada ka damu.  Ka dai tabbata kana da “Data” isasshe a kan makalutun sadarwarka (Modem), domin masarrafar za ta koma kwamfutocin kamfanin Bluestacks ne dake Intanet, don loda wadannan jakunkunan bayanai.
Idan ta gama, za ta bude maka masarrafar “Play Store” irin wannan da ka sani na Android, amma ba za ka iya komai ba sai ka sa sunanka (username) da kalmar iznin shiga (password) na manhajar Imel din Gmail kenan.  Idan ba ka dashi, akwai inda za ka matsa don yin rajista nan take, babu matsala.  Matakan ba su da wahala.  Idan ka gama rajista, sai kaje wajen “Applications” ka matsa tambarin “Search” dake bangaren hagu daga sama, ka rubuta “Whatsapp” ko duk manhajar da kake son amfani da ita a kan kwamfutarka, ka matsa “Enter” a allon shigar da bayananka, nan take za a budo maka su yarbatsai, ka zabi wanda kake so, sai ka loda.  
Idan ka gama loda manhajar, sai ka bude, daga nan kuma za ta bukaci kayi rajistar layinka kamar dai yadda ka san ake yi a wayar salula.