✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Game da zancen gwajin jini kafin aure musamman gwajin birbishin ciwon sikila. To idan saurayin da budurwar kwata-kwata babu tarihin cutar a danginsu fa? Za…

Game da zancen gwajin jini kafin aure musamman gwajin birbishin ciwon sikila. To idan saurayin da budurwar kwata-kwata babu tarihin cutar a danginsu fa? Za su iya aure ba gwajin?

Daga Husmila M., Kazaure

 

Amsa: Ko da a iyaye da kakanni da sauran dangin saurayi da budurwa ba a taba jin tarihin mai ciwon sikila ba, wajibi ne idan ana so a kaucewa samun ‘ya’ya marasa ciwon sikila a yi wannan gwaji na ‘Hb genotype’ kafin aure. Dalili kuwa shi ne idan da tun farko kin gane cewa akwai masu dauke da matsalar wadanda ba sa nunawa a fili karara su sikila ne, da baki yi ma wannan tambaya ba. Don haka a dangin saurayin ko na yarinyar, ko ma a jininsu su kansu, za a iya samun masu dauke da ciwon (wato rabin ciwon da ke cewa AS) wanda bai bayyana a matsayin ciwon sikila ba, amma za su iya sa wa ‘ya’yansu. 

Abu dai mai faranta rai ga mu ma’aikatan lafiya masu hakilon ganin an kakkabe irin wadannan cutuka a al’umarmu nan gaba kadan, shi ne ko kun fahimta ko ba ku fahimta ba, kun ga yanzu dai ku mutan Kazaure ba ku da zabi sai kun yi wannan gwaji kafin aure tunda ya zama doka a jiharku.

 

Mace mai jego da ta haihu bayan makonni biyu za ta iya yin doguwar tafiya kamar daga Kudu zuwa Arewacin kasar nan?

Daga Bashar Muhammad Ikko

 

Amsa: E, in dai ba ta jigata ba lokacin haihuwar, kuma tafiyar da za ta yi ba za ta jigatar da ita sosai ba, kamar idan a jirgin sama za a je, ai ba matsala sosai. Sai dai an fi so idan ba wani uzuri ba ne na gaggawa a bar ta sai bayan makonni shida wato sai ta yi ‘arba’in’.

 

Kamar iya yawan wadanne shekaru ne ake son matar da ta haihu a ce ta huta kafin ta samu wani sabon cikin? Domin ni ina sha’awar matata ta huta saboda wasu dalilai.

Daga Idris Baban Abba

 

Amsa: Ai sai ran da ka ga ta yaye jaririn karshe ya fara cin abinci sosai, kuma ita ma ta nutsu ba ta shan wata wahalar raino, kuma jikinta ya murmure, wanda zai iya daukar shekaru biyu zuwa uku. Amma tunda ka ce kana da dalilinka, to ya danganta da dalilin naka. Misali matarka ce ta samu karatu a makarantar da sai ta shekara uku ko hudu kafin ta kare, kuma karatun na bukatar nutsuwa sosai. To idan kana so ka ba ta lokaci har sai ta gama, ka ga sai ku nemi dabara ta hutun shekaru uku zuwa hudun kenan.