Likita, na je an yi mini hoton scanning ne a ciki sai aka ce kitse ya lullube mini hantata, shi ne nake tambaya ko shi ke nan ina da ciwon hanta ke nan? Kuma mene ne magani?
Daga Talatu, Kaduna
Amsa: E, za a iya kiransa ciwon hanta kai tsaye, tunda a likitance ma haka ake kiran matsalar, wato fatty liber disease. Amma sai dai shi yana iya warkewa sarai, ba kamar sauran matsalolin hanta ba. Wannan kan faru a mata masu kiba sosai, ko wadanda suka yi kibar suka zo suka zabge tashi guda. Kitse kan shiga ko’ina ya yi zamansa a masu kiba, amma tunda da dama a hanta ake sarrafa shi, wasu idan aka sarrafa su sai su yi zamansu a nan, har su fara takura wa aikin hantar. Akan samu ma a mata masu juna biyu lokacin da cikin ya fara tsufa, su ma musamman idan suna da kiba. A maza kuma banda masu kiba, an fi samu a masu shan barasa. Shan wasu magunguna ma kamar irinsu sha-ka-fashe, ko na matsalar kanjamau, za su iya kawo wannan matsala.
Da yake baki fadi dalilin da ya sa kika je yin hoton ba, dama kusan ita wannan matsala ba wasu alamu take zuwa da shi ba, sai dai kawai idan an je aune-aune da bincike-binciken lafiya a gano shi a scanning din.
A mafi yawan lokaci daina cin maiko yana taimakawa kwarai da gaske wajen maganin wannan matsala. Wannan ya zama dole saboda ko mutum bai ci maiko na abinci ba, ita hantar dai dole ta sarrafa shi daga sugan da muke sha. Don haka idan kina da kiba, a yanzu kaurace wa maiko ita ce shawara ta farko, ko ki rika amfani da man zaitun kacal maimakon saura ire-iren man abinci. Da fara neman hanyoyin rage kiba a hankali-a-hankali, ba tashi guda ba, kamar motsa jiki. Wannan ne zai kona kitsen ba na hanta ba, har ma sauran sassan jiki. Haka ma ga mai shan barasa, daina shan barasa kan iya sa abin ya warke.
To amma ba za a tsaya a nan ba, dole kuma sai an je asibiti an tuntubi likitocin kayan ciki wato GIT wadanda za su ba da sauran gwaje-gwaje da sauran shawarwari, idan ma ta kama a ba da wadansu magunguna masu kona wannan kitse.