✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Alamun nakuda Wadanne alamu ne mace mai juna biyu za ta rika ji idan ta kusa haihuwa?   Amsa: Akwai alamu da mace da ta…

Alamun nakuda

Wadanne alamu ne mace mai juna biyu za ta rika ji idan ta kusa haihuwa?

 

Amsa: Akwai alamu da mace da ta cika watanni tara za ta fara gani idan ta karato lokacinta. Wadannan alamu sukan ma fara tun kafin mara ta fara ciwo, wato kafin mahaifa ta rika daurewa tana takurewa ana jin zafin nan. Idan lokaci ya zo sai bakin mahaifa ya fara budewa. Sakamakon haka abu na farko da mace za ta gani shine zubar wani dan ruwa da yake bakin mahaifa, mai kamar majina. Wato shi ba jini bane, shi kuma ba tsinkakken ruwa ba. Wannan ne ke ba mahaifa damar fashewa, wanda ake cewa ‘fashewar faya’. Sauran abubuwan da za ta ji sune ciwon mara, ciwon baya da jin karuwar nauyi a mara. 

To daga wannan lokaci zai iya daukar awa guda zuwa ‘yan kwanaki kafin babbar nakudar ta zo.

 

Matata ce ke da ciki wata uku amma har yanzu ba ta daina ganin jini ba. Ta je asibiti an duba ta an ba ta magani amma har yanzu bai daina ba. Ko mece ce mafita?

Daga Ibrahim M.

Amsa: Da ma dai ka riga ka san ai bai kamata a samu zubar jini a mai juna biyu ba, wanda shine ma ya sa ka yi wannan tambaya. To amma duk da haka akan iya samun ‘yan matsaloli da za su kawo zubar jini a watannin farko na ciki, musamman watanni uku na farko. Wadannan matsaloli sun hada da rashin samun isasshen hutu, ko rashin cin abincin da zai wadaci ita mai juna biyun da abinda ke ciki, ko kuma shigar kwayoyin cuta jikin uwar kamar na zazzabin maleriya ko na zazzabin mafitsara, wadanda sune aka fi gani a masu juna biyu. To tunda ta je asibiti kuma sun duba sun ce ba matsala sun kuma ba da magani, abin da sauki kenan, musamman ma idan sun yi hoton scanning sun nuna mata harbawar zuciyar jaririn, alamar komai lafiya kenan. Watakila kawai sai dai su kara da cewa ta daina aikace-aikacen gida kwata-kwata sai ta haura watanni uku, kuma jinin ya daina zuba sa’annan za ta ci gaba.

 

Wai shin wane irin gwaji ne akan yi wa uba da dansa, wanda zai tabbatar cewa dan nasa ne?

Daga Maman Walida

Amsa: Akwai gwaje-gwaje masu dama da sauki wadanda za a iya yi wa da da uba a binciki ko suna da wata alaka ta jini. Wadannan gwaje-gwaje sune irinsu na ajin jini amma kusan a yanzu an daina daukarsu a matsayin sahihai. Wanda ya fi zama dahir shine gwajin kwayoyin halittu na DNA, wato DNA profiling, wanda kusan ba ja idan ya ba da sakamako a iya cewa kusan kashi 100% cikin dari ba kuskure.