✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

  Na ga bayanink a kan yara masu jijjiga. Ni ina da yaro amma yanzu ya kai shekaru 30 yana samu jefi-jefi bai daina ba.…

 

Na ga bayanink a kan yara masu jijjiga. Ni ina da yaro amma yanzu ya kai shekaru 30 yana samu jefi-jefi bai daina ba. Wane asibiti ya kamata mu je?

Daga Halima, Lafiyar Barebari

Amsa: Ga alama ba ki fahimci zancen ba, wanda aka yi shi gwari-gwari har Barebari ma su iya fahimta. Ya kamata ki sake daukar jaridar ki duba, saboda an rubuta karara akwai bambanci tsakanin jijjiga wadda zazzabi kan jawo da ta ciwon farfadiya. Yaron da ya wuce shekaru biyar yana samun jijjiga jefi-jefi matsalarsa ta fi kama da ta farfadiya, balle ma yanzu kin ce shekarunsa 30. Wani bambancin kuma shine jijjiga ta zazzabi tana tafiya amma farfadiya har yanzu ba maganin waraka a likitance, sai dai maganin rage kaifin ciwon.

Idan kika kai shi babban asibiti a nan Lafiya ko Jos ko a Abuja bangaren kwakwalwa, za a duba shi a gani ko farfadiyar ce, a bashi irin magungunan da za su rage yawan tashin ciwon.

 

Mene ne maganin beli? Ina da yaro da nake so a cire masa na kira wanzami ya kasa. Yaron ya kai shekaru bakwai

Daga Ilyas, Suleja

Amsa: To ku ‘yan Suleja har yanzu ba ku daina ba wanzami cire beli ba? Tabbas aikinsu ya fi araha, amma ai zamani ya ci gaba. Mu dai nan birni tuni muka waye, wanzami sai dai gyaran fuska. Maganin beli a zamanance sai mu ce ka tuntubi likitan hanci da makoshi wato ENT wanda zai duba ya ga ko me ya samu belin yaron, ya masa magani ko ma tiyata.

 

Ni kuma yarinya ta ce duk shekara lokacin zafi sai ta yi kuraje a goshi wasu lokuta masu ruwa, wasu lokuta kuma kanana masu kaikayi. Mu jejje asibiti an ba da magani, idan sun warke sai su dawo. Shine muke neman shawara

Daga Mustapha H., Kano

Amsa: To su wadanda suke ruwa da alama sune wadanda kwayoyin cuta suka shiga kamar maruru, su kuma marasa ruwan kamar sune na zafi, wadanda suke fitowa saboda yawan zufa.

 

Shin ya dace macen da take da juna biyu ta yi amfani da magani Aspirin ko mai dauke da ayarin shi Aspirin din?

Daga Yaana Garba, Gashua

Amsa: A’a bai dace mace mai juna biyu ta yi amfani da Aspirin ko mai dauke da ayarin Aspirin ba, domin shi Aspirin tsinka jini yake, ita kuma mai juna biyu ba a so jininta ya tsinke don kada ta samu zubar jini a mahaifa. Sai dai kwararrun likitoci a wasu yanayi na rashin lafiya za su iya rubuta mata idan ya zama dole, kamar a mai ciwon zuciya ko mai hawan jini wadda ake kokarin karewa daga samun jijjiga, shi ma sai ana yi ana yawan bibiyar jinin.