✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da intanet

Assalamu alaikum Baban Sadik, tsawa lokacin ruwan sama a mahangar Musulunci, an ce tasbihin Mala’iku ne. To meye dalilin tsawa a mahangar Malaman kimiyya?  Wa…

Assalamu alaikum Baban Sadik, tsawa lokacin ruwan sama a mahangar Musulunci, an ce tasbihin Mala’iku ne. To meye dalilin tsawa a mahangar Malaman kimiyya?  
Wa alaikumus salam. Ba ni da tabbaci kan zancenka na farko kan dalilin samuwar tsawa a mahangar Musulunci, cewa tasbihin Mala’iku ne.  Amma dangane da iyakar bincike, malaman kimiyya sun nuna kafin samuwar tsawa, akwai haske da ke bayyana, wato walkiya ke nan, kamar yadda muke cewa, daga nan sai samuwar rugugi mai karfi mai girgiza da muke kira cida a harshen Hausa, bayan cida ne kuma sai sautin tsawa ya biyo baya a karshe.  Haka abin ke biye, kamar yadda muke ji ko gani.  Amma a hakika, lokaci guda duk suke samuwa.  Mene ne dalilin samuwar tsawa?  Yaya walkiya da rugugin cida ke rigar sautin tsawa?  Wannan tambaya, irin ta aka yi wa Farfesa Richard Brill da ke Kwalejin Honolulu (Honolulu Community College) a kasar Amurka, cikin shekarar 2000, Mujallar “The Scientific American” ta buga a shafinta a watan Disamba na shekarar 2002.  Ga nassin amsar da ya bayar nan kai tsaye na fassaro maka:
“Abin da ke haddasa samuwar tsawa shi ne walkiya, wanda asali yake dauke da  cunkoson sinadaran “Electron” da ke makare a cikinsa ko a tsakanin giragizai, ko kuma tsakanin giragizai da mahallin da muke rayuwa a ciki a wannan duniya tamu.  Nau’in iskar da ke gewaye da wadannan sinadaran “Electron” kan yi zafi (sanadiyyar zafin rana), zafi mai tsananin da ya kai kimanin digiri 50,000 a ma’aunin zafi na faranhait (50,000F), daidai da zafin rana ninki uku ke nan.  Da zarar wannan iska mai dan karen zafi ta fara hucewa, sai ta samar da wata jakar iska a gewaye da titin da iskar ke bi.  Nan take sai iskar da ke makwabtaka da wannan jakar iska ta rika fadada tana tsukewa, tana fadada tana tsukewa (edpansion and contraption), lokaci-lokaci.  Wannan ke sa jakar iskar da ke gefe ta rika girgiza cikin batsewa, hakan kuma yana haifar da sautin tsagewa.  Da zarar wannan girgiza ta fara lafawa, sai ta haifar da wani sauti mai tsakanin kara da muke kira Tsawa.
Muna iya jin masifaffen sautin tsawa da bugawarsa daga tazarar mil goma (kilomita 13) ko sama da haka daga hasken da ke haddasa tsawar.  Sannan idan walkiya ta auku a iyakar tazarar da ake iya ganinta, ita muke fara gani (ba sautin rugugin cida ko tsawar ba), domin gudun sauti a cikin haske bai kai gudun sinadaran “Electron” da gudanuwarsa ba. Shi ya sa ma sautin tsawar ke aukuwa kamar sautin hatsarin wutar lantarki (Shockwabe), ba kamar sauti irin wanda da aka sani na al’ada ba.  Shi wannan sauti mai kama da sautin hatsarin wutar lantarki yana bibiyar titin wannan sinadarin “Electron” ne (a yayin da yake aukuwa) kamar yadda dunkulen yatsu ke tasiri a jiki yayin da aka naushi mutum.
Bayan haka, gudun sauti ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da gudun haske.  Hasken da ke samuwa a yayin walkiya na riskarmu ne (a wannan duniya) cikin kasa da dakika (second) guda, a yayin da sautin ke biye da shi cikin saibi da nawa, kai ka ce dodon kodi ne ke biye da jirgi nau’in roket da ke shawagi a tsakanin duniyoyi.  Don haka, yanayin sauti da haske da ke samuwa a lokacin walkiya da tsawa hadaka ne na abin da ke samuwa sanadiyyar girgizar da sinadaran iska ke yi wajen hargitsa karfin sinadaran lantarki.  Wannan wani al’amari ne mai matukar ban mamaki hakika, kuma wannan ke daka tunatar da mu duka cewa mu ba komai ba ne idan aka gwama halittarmu da ta sararin samaniya.”

Salaamun alaikum, don Allah yaya zan yi in bude Mudawwana (Blog Page). Saboda ina son zama “Blogger.” –  Mubarak El-anwar, Kano
Wa alaikumus salaam.  Bude shafin Mudawwana ko Taska, abu ne mai sauki.  Ka je daya daga cikin gidajen yanar sadarwa da ke da manhajar shafin Mudawwana a Intanet, misali, WordPress (www.wordpress.com) ko kuma na kamfanin Google mai suna Blogger (www.blogger.com) don yin rajista.  Idan ka tashi yin rajista, za a bukaci adireshin Imel.  Idan na Blogger ne, dole sai kana da adireshin Imel na kamfanin Google, wato Gmail ke nan.  Kana iya yin rajista a http://mail.google.com kyauta. Idan kuma na kamfanin WordPress ne, duk adireshin Imel din da ya sawwaka kana iya amfani da shi.  
Bayan ka yi rajista, za a zarce da kai zuwa shafinka, daga nan sai ka sanya shi yadda kake so, ka ci gaba da zuba dukkan ra’ayoyinka.  Dangane da zama “Blogger” kuma, wato Marubuci na musamman a Mudawwana, wannan abu ne mai sauki, muddin za ka juri rubutu da karanta ra’ayoyin wasu da yawo cikin duniyar ilimi kan fannin da kake da sha’awar rubutu ko zama “Blogger” a kai.  Allah sa a dace, Ya kuma sa a dabi’antu da juriya da hakuri, amin.

Baban Sadik, da fatan kana lafiya, Allah Ya kara maka basira.  Ni ma’abocin sauraron gidanjen rediyo ne.  Hakan ya sanya nake kokari wajen tura sakonnina domin in bayyana ra’ayina, amma abin takaici ba su karanta sakonnina, duk cewa suna nuna sun isa wato “Delibered”; duk da kokarin da nake yi wajen kyautata rubutuna. Don haka nake son ka ba ni shawara. Na gode. – Bello Isiyaku, Birnin-Fulani
Barka ka dai Malam Bello.  In na fahimci sakonka da kyau, kana nufin a duk sadda ka tura sakonninka, wayarka na sanar da kai cewa sakon ya isa.  Amma kuma ba a karanta sakonninka.  Eh to, tunda har waya ta sanar da kai cewa sako ya isa lafiya, ba na tunanin akwai matsalar yanayin sadarwa, wato Network Problem, ta yiwu tambayoyin naka ne ba su gamsar da su ba; ko ba su zo kan sakon naka ba, saboda yawaitar sakonnin da suke karba; ko kuma akalla ba su cika ka’idar da suka gindaya ga sakon da ya cancanci a karanta shi ba, kafin amsa shi. Ko kuma, a karo na karshe, watakila sun sha amsa tambayoyi makamantansu a baya.  
Ta kowane hali dai, dole ne ya zama akwai dalili mai karfi wanda kuma, kamar yadda ka sani, ba abu ba ne mai yiwuwa su iya sanar da dukkan masu turo sakonni dalilin rashin karanta sakonninsu.  Sai dai in ce ka ci gaba da kokari da kuma juriyar aikawa, watakila nan gaba za a dace su karanta.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum, da fatan alheri gare ka kuma ka yi sallah lafiya, amin.  Allah Ya raya mana iyali su zama masu albarka.  Bayan haka, don Allah Baban Sadik, ina so a yi min karin haske; ina so na koyi sana’ar abin da ya shafi gyara babbar manhajar wayar salula (Mobile Operating System Formatting) da filashin manhajar, da kuma yadda ake bude babbar manhajar idan ta kulle, ta hanyar kwamfuta.  Wace hanya zan bi?  Sannan dole ne sai na shiga makarantar koyon kwamfuta?  A cikin bayanin takaitaccen tarihin rayuwarka, na ji ka ce da jangwale-jangwale ka koyo ta, wato kwamfuta ke nan.  Sannan ina so in sani, ko ban je makarantar kwamfuta ba, zan iya sarrafa ta a aikace?  Da fatan za ka daure ka ba ni amsa.  –  Yahuza Idris, Hotoron Arewa.
Wa alaikumus salam, Malam Yahuza.  Ina godiya matuka da addu’o’inku, Allah saka da alheri, amin.  Koyon wannan sana’a abu ne mai kyau matuka, musamman ganin cewa babu abin da ya fi yaduwa a al’ummarmu yanzu daga cikin kayayyaki ko na’urorin sadarwa irin wayar salula.  Don haka, koyon yadda ake gyara su, da gano matsalolin da ke addabarsu, abu ne mai matukar mahimmanci, bayan samar da aikin yi ga matasa.  
Koyon wannan sana’a, ko fannin ilimi, ba wani abu ba ne mai wahala, matukar mai koyo ya sa hankali da ransa a kan lamarin.  Akwai wurare da dama da ake koyar da gyaran wayoyin salula.  Akwai cibiyoyin koyar da sana’o’i da gwamnatocin arewacin kasar nan da dama suka samar, karkashin shirin gwamnati na samar wa matasa abin dogaro da kai.  Idan ba ka samu damar shiga wadanann cibiyoyi ba, akwai masu gyaran wayoyin salula kamar yadda muke da masu gyara rediyo da talabijin, birjik.  Daga cikinsu akwai masu gyara babbar manhajar wayar salula ta amfani da masarrafar filashin din wayar salula, wato “Mobile Phone Flashing Software.”  Kana iya shiryawa da su, ka biya su kudin hidimar karantar da kai da za su yi, sannan su karantar da kai.
Da zarar ka gama wannan karatu, dole ne ka mallaki kayayyakin aiki, wanda na san malaminka zai sanar da kai.  Za ka bukaci kwamfuta, musamman dai ta tafi-da-gidanka, wato Laptop ke nan, da dukkan abin da zai sawwake maka mu’amala da ita.  Sannan za ka mallaki masarrafa ko manhajar da ake yin filashin din babbar manhajar wayar salula, kamar yadda bayani ya gabata a sama.  Wannan masarrafa na zuwa ne da wayoyin USB da ake makala su a jikin wayar da za a mata filashin don riskar babbar manhajar.  Dole ne su karantar da kai cewa kowane kamfanin wayar salula yana da nasa nau’ukan wayoyin USB.  Nokia da nasu.  Samsung da nasu.  Sony da nasu, har dai zuwa karshe.  Bayan haka, za ka mallaki manhajar bude wayar salular da ta kulle kanta ko mai ita ya kulle ta cikin kuskure ko ya mance kalmomin sirrinsa ko isharar da ake bude wayar da ita, wato “Security Lock Pattern” ke nan, ga nau’ukan wayoyi masu amfani da babbar manhajar Android.  A takaice dai, dukkan kayayyakin aiki za ka mallake su kafin fara aiki.
Dangane da tambayarka kan ko mutum na iya mu’amala ko sarrafawa ko kuma koyon kwamfuta ko da bai yi karatun boko ba, sai in ce maka eh, mutum na iyawa.  Abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  A wajen koyon wancan ilimi ko sana’a, dole za a koya maka yadda ake mu’amala da kwamfuta da yadda za ka sarrafa ta wajen aiwatar da dukkan ayyukan da ake so.  Har wa yau ka fahimci wani abu daya, shi ilimin kwamfuta na da bangare biyu ne; akwai bangaren karatu da nazari.  Sannan akwai bangaren aikata karatun a aikace.  Kowannensu yana da mahimmanci, musamman bangaren aikata karatun a aikace.  Domin kana iya mu’amala da kwamfuta ko ba ka taba zuwa makaranta ba.  Amma ba za ka taba iya samun shaidar karatu a fannin kwamfuta ba tare da ka je makaranta ba.  Kamar yadda ka ji na fada a baya, ban taba zuwa makarantar koyon ilimin kwamfuta ko wayar salula ba a rayuwata.  Duk da cewa ban fid da rai da hakan ba nan gaba, saboda wasu dalilai da suka shafe ni.  Amma a tare da haka, iya gwargwado, na fahimci wannan ilimi fiye da tunanin wanda ya je jami’a ya kware a wannan fanni.  A hakan da nake, ina sa ran zan iya karantar da ko da ’yan jami’a ne, kan wannan ilimi na fannin kwamfuta.  Abin da kake bukata shi ne, ya zama kana da sha’awar lamarin, sha’awa mai karfi, ba mai rauni ba.  Na biyu, ka yawaita mu’amala da kwamfuta.  Na uku, ka yawaita tambaya da neman karin bayani wajen kwararru kan wannan fanni.  Na hudu, ka samu wanda zai rika koya maka yadda ake mu’amala da wannan na’ura ta kwamfuta a aikace.  Duk wanda zai koya maka amfani da wannan na’ura, zai koya maka ne kamar yadda ake karantar da ita a rubuce.  Don haka, duk wanda ya ga kana mu’amala da kwamfuta bayan ka kware, zai dauka makaranta ka je ka koya.  Me ya sa?  Don wanda ya je makarantar ne, ko wanda ya koye ta a karance ne ya karantar da kai.  Da fatan ka gamsu da wannan dan gajeren bayani.   
Za mu ci gaba.