✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da Intanet (2)

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan an yi sallah lafiya.  Wai don Allah akwai wata manhajar kwamfuta mai suna “Data Analysis?” –  Abdullahi Bashir DawudWa…

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan an yi sallah lafiya.  Wai don Allah akwai wata manhajar kwamfuta mai suna “Data Analysis?” –  Abdullahi Bashir Dawud
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Abdullahi. Kalmar “Data Analysis” wani fanni ne na musamman da ya kunshi neman bayanai da tattaro shi da kintsa shi da tace shi da kuma tsara shi yadda ake so don samar da natija ko bayar da damar yanke hukunci kan sakamakon da bayanan suka bayar.  Ba wai sunan wata manhaja ba ce.  Sai dai kuma, akwai manhajojin kwamfuta masu dimbin yawa da aka gina su don aiwatar da wannan aiki mai matukar fa’ida a wannan zamani namu.  Ire-iren wadannan manhajoji ana amfani da su a ma’aikatu da masana’antun gwamnati da makarantu da kuma gama-garin mutane masu sha’awar wannan fanni, don aiwatar da wadancan ayyuka da na zayyana a baya.  Daga cikin wadannan manhajoji akwai manhaja mai suna “R”, da “SPSS” (Statistical Package for Social Sciences) wanda galibin daliban jami’a ke amfani da ita wajen nazarin bayanan da suka tara yayin gudanar da bincikensu, sannan akwai kanana irin su “Microsoft Edcel” na kamfanin Microsoft, wadda shahararriya ce.  Kamar yadda na ce a sama, ire-iren wadannan manhajoji suna da yawa, sun kai dari, kuma idan dalibi ya koyi mu’amala da su wajen nazarin bayanan da ya tara a yayin gudanar da bincikensa, suna taimaka masa matuka.  Domin da zarar ka tsamo bayanai masu mahimmanci da kake son yin nazari kansu, kana aika wa manhajar ka matsa maballi guda, nan take za a tace bayanan, a turo maka amsa kai tsaye wadda za ta ba ka haske kan abin da kake nema.  Da fatan ka gamsu da wannan gajeren amsa nawa.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, mun gode da yadda ake agaza wa jama’a.  Don Allah, zan iya yi wa kwamfuta “Formating,” in eh, yaya ake yi?  Sannan yaya zan yi in mayar da babbar manhajar “Windows 7” zuwa “Windows 8?”  Na gode, Allah kara maka fahimta.  – Mishary Mishary
Wa alaikumus salam, barka da warhaka. Yadda ake “Formating” kwamfuta ko babbar manhajar kwamfuta ba abu ba ne da bayaninsa zai gamsar a nan.  Domin na farko ba ka ambaci nau’in babbar manhajar ba.  Na biyu ba ka ambaci ko hakikanin manhajar da kwamfutar ta zo da ita ne ko kuma daga baya ne aka sanya wa kwamfutar ba.  Na uku, ba ka ambaci nau’in babbar manhajar da za ka sa mata ba, idan ka goge wadda ke ciki.  A tare da haka, kalmar “formating” na ishara ne ga tsarin maye gurbin wata babbar manhajar kwamfuta da wata daban, ko da irinta ce.  A tsarin “Formating” idan aka maye gurbin wata babbar manhaja da wata, komai na gogewa ne, sai sabuwar babbar manhajar da aka sa ce za ta tabbata.  
Kafin a yi “Formating” babbar manhajar kwamfuta, yana da kyau ya zama an bi dukkan hanyoyin da za a iya bi wajen gyara babbar manhajar da ke cikin kwamfutar.  Sai in an rasa wata hanya ce sannan za a yanke hukunci na karshe.  Domin da zarar an yi “Formating,” to kwamfutar ta dawo kamar sabuwa ce.  
Idan kwamfuta ta rikice, yana da kyau a bibiyi hanyoyin gyara.  Misali, idan tana saibi ne, ba ta sauri a duk sadda aka ba ta umarni, wannan alama ce da ke nuna abubuwa da dama, musamman idan a baya ba haka take ba.  Da farko sai a duba babbar ma’adanarta (Hard Disk Dribe) watakila ta cushe ne, ma’ana ta kusan cikewa ko ma ta cike.  Idan akwai sauran wuri a ma’adanar isasshe, sai a duba ma’adanar wucin-gadi, wato “RAM” ke nan.  Ita ma muddin ta yi karanci, babu yadda za a yi kwamfutar ta tafi daidai.  Domin ita ce ma’adanar da ke samar wa sauran manhajoji wurin zama da zarar ka kira su don yin amfani da su.  Idan wannan ma’adana ta yi karanci ne (watakila ba ta wuce 1GB ba, alhali tana dauke ne da Windows 7 misali), duk sadda ka kira wata manhaja da kyar za ta budo, domin babu isasshen wurin zama.  A nan dole ne a kara mata ma’adanar RAM zuwa a kalla 2GB, ko a yalwace 4GB.  Abu na gaba da ke iya sa kwamfuta ta rika saibi shi ne samuwar kwayoyin cutar kwamfuta, wato “Computer birus” ke nan.  Wannan ana iya magance shi ne ta hanyar tace dukkan bayanan da ke kwamfutar kai tsaye, ba tare da bata lokaci ba.  Wannan shi ake kira “Scanning” a Turance.  Haka idan kwayoyin cutar kwamfutar sun yi mummunan tasiri a kan bayanan babbar manhajar ta yadda ba ta iya aiki yadda ya kamata sanadiyyar goge su da ta yi ko wani abu makamancin haka, ana iya “gyara” babbar manhajar kwamfutar ba tare da an goge ta ba.  Wannan tsari shi ake kira “Repair.”  Ana iya hakan ne ta hanyar amfani da faifan CD din babbar manhajar, kwamfutar za ta kashe kanta ta sake kunnuwa, daga nan za ta loda dukkan bayanan da suka goge, sauran kuma ta bar su yadda suke, sai a gyara babbar manhajar cikin sauki.  Don haka, sai an bi matakai makamantan wadannan, an rasa mafita, sannan a fara batun “Formating.”
Idan bukata ta kama a maye gurbin wata babbar manhaja da wata, ana iyawa.  Sai a kwashe bayanan da ke ciki masu amfani in zai yiwu.  Idan ba zai yiwu cikin sauki alhalin tana kunne ba, ana iya kashe ta, sai a cire babbar ma’adanar kwamfutar, a jona ta da wata kwamfutar ta amfani da wayar USB, don kwashe bayanan da ke ciki, cikin sauki.  Bayan nan, sai ka shiga gidan yanar sadarwar kamfanin da ya kera kwamfutar don nemo dukkan kananan masarrafun da ke hada alaka a tsakanin babbar manhaja da gangar-jikin kwamfutar.  Wadannan kananan masarrafu su ake kira “Driber Softwares,” domin idan ka maye waccan babbar manhaja mai matsala da wata sabuwa, dole sai ka maye gurbin wadannan kananan masarrafai, in ba haka ba, kwamfutar ba za ta iya kada sauti ba, ko nuna hoton bidiyo, ko iya shiga Intanet.    In ka gama samunsu, sai ka adana su a bangare guda.  
Abu na gaba shi ne, sai ka samo faifan CD da kwamfutar ta zo da shi.  Idan babu, sai a dauko ma’adanar da aka taskance babbar manhajar da ita (idan an yi ke nan).  Idan duk babu wannan, ana iya samun wani faifan CD sabo irin na babbar manhajar da ake son mayewa.  Tunda sabon zubin babbar manhaja za a yi mata yanzu, wato “Fresh Installation.” Bayan samun wannan faifan CD, sai a jona kwamfutar da wutar lantarki kai tsaye.  Ba a “Formating” kwamfuta idan tana kan batir, ko da kwamfutar tafi-da-gidanka ce, wato Laptop.  Sai a sanya faifan CD a cikin kwamfutar, a kunna.  Da zarar ta fara tashi, za ta hangi wannan faifan CD, sai ta loda shi.  Da zarar ta loda, za ta fara sarrafa bayanan da ke ciki kai tsaye.  Sai ka bi ta a hankali, za ta rika yi maka tambayoyi kana ba ta amsa. Za ta goge babbar manhajar da ke ciki ne gaba daya, sai ta loda sabuwa, sannan ta ba ka damar tsara sabuwar babbar manhajar wajen shigar da sunanka da kalmar iznin shigarka da kasarka da lokaci da kwanan wata da dai sauransu.  Idan ta gama, za ta kai ka shafin farko, wato “Desktop” ke nan.  Daga nan sai ka loda mata dukkan kananan masarrafan da ka nemo daga gidan yanar sadarwar kamfanin da ya kera kwamfutar, wato “Driber Softwares” ke nan, nan take za ta dawo sabuwa ful,  zan-zan.
Batun juya babbar manhajar “Windows 7” zuwa nau’in “Windows 8” kuma matakansa daban ne.  Da farko dai dole ne ya zama babbar manhajar da ke kwamfutar ta asali ce, wato orijina, wacce kwamfutar ta zo da ita ko wadda aka loda daga faifan CD na asalin kwamfutar, ba irin na bogi wadanda ake sayarwa a bakin titi a biranen kasar nan ba.  Ko wadanda ake saukarwa daga Intanet na bogi (Pirated) ba.  Domin illar wadannan nau’uka na bogi shi ne da zarar ka fara amfani da babbar manhajar, har wata munasaba ta fuskantar da akalarka zuwa shafin kamfanin Microsoft da ke Intanet, nan take za su gane cewa jabu ce, kuma duk wasu kare-karen tagomashi da ake baiwa babbar manhajar Windows ta hanyar Update ba za ka same su ba.   Wannan zai jefa kwamfutar cikin hadari, ta yadda a karshe, rashin wadancan kare-karen tagomashi na iya sa ta kamu da kwayoyin cutar kwamfuta.  Ba wannan kadai ba, kafin ka juyar da Windows 7 zuwa Windows 8, dole ne ka yi abin da ake kira “Compatibility Test” ta hanyar loda wa kwamfutarka wata manhaja karama daga shafin Microsoft da ke Intanet, don auna mizani, da tsari, da kintsin kwamfutarka ko za ta iya daukar sabuwar manhajar Windows 8 ba tare da matsala ba.  Da kuma nau’ukan masarrafan da ke kwamfutarka a yanzu wadanda ba za ka iya amfani da su ba a Windows 8.  Domin akwai bambancin tsari da kintsi sosai a tsakanin Windows 7 da Windows 8.
Bayan ka tabbatar da ingancin babbar manhajar da ke kwamfutarka, sai ka jona ta da Intanet, ka nemo bayanan karin tagomashi, wato “Windows Update”. Kana iya haka ta hanyar latsa “Start” ka je “All Programs” sai ka gangara “Windows Update,” ka latsa, shafi zai budo.  Sai ka matsa “Check for Updates.”  Za ta nemo dukkan bayanan da kwamfutarka ke bukata.  Idan ka gansu, sai ka matsa “Install Updates,” don loda wa kwamfutar.  Haka za ka yi ta yi, har sai an ce maka “Your Computer is Up to Date.”  Daga nan sai ka shiga shafin Microsoft da ke Intanet (www.microsoft.com) ka je sashen Windows 8, ka matsa alama mai take: “Run Windows 8 Compatibility Test.”  Idan ta gama wannan bahasi, kamar yadda na zayyana a sama, za ta sanar da kai manhajojin da ba za su yi amfani ba a sabuwar babbar manhajar.  Wannan matakin farko ke nan.
Sai ka nemo faifan CD mai dauke da babbar manhajar Windows 8 ka loda wa kwamfutar, ka sake kunna ta, wato “Restart” ke nan.  Babbar manhajar za ta gudanar da sauran ayyukan, tana neman bayanai daga wajenka kana ba ta.  Ba wai barinta za ka yi kawai ta yi ta yin kidinta da rawanta ita kadai ba.  Akwai inda za ta kai ta saurare ka don ba ta bayani.  Idan ba ka kusa, haka za ta tsaya cif, ba gaba ba baya.  Ka ga idan ba ka kusa da matsala ke nan.  Idan ta gama za ta sanar da kai, sai ka tsara ta yadda kake so.  Za ka ga shafin farkonta ya sha bamban da na Windows 7.  Maimakon budo maka shafin farko (Desktop), za ta budo maka “Start Page” ne, mai dauke da sabuwar fuskar babbar manhajar.  Allah sa a dace.
Za mu ci gaba.