✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da Imel (4)

A yau mun ci gaba ne na amsoshin tambayoyinku.  Tambayar ta yau kwara daya ce rak, saboda nauyin bayanin da ke tattare da ita.  A…

A yau mun ci gaba ne na amsoshin tambayoyinku.  Tambayar ta yau kwara daya ce rak, saboda nauyin bayanin da ke tattare da ita.  A sha karatu lafiya.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, na lura idan aka sa duwarwatsu da ruwa kamar kofuna uku a cikin tayar mota, ko kuma tif (tube), aka kuma tayar da motar aka fara tafiya da ita, tayar za ta rika jujjuyawa ne kamar yadda duniyarmu take zagaya rana, sannan wadannan duwarwatsun za su rika yawo ne a hargitse; wannan ya hau wannan, wancan ya hau wancan – babu kan-gado.  Tambayata a nan ita ce: me yasa duniyarmu da karikitan da ke cikinta – kamar su tekuna, da gidaje, da motoci ba su irin wannan garwayar?   Kuma me yasa ba mu ganin kanmu ya koma kasa kafafunmu sun koma sama; sai ka ga komai a natse?  Alhali kuma idan ka jera gwangwanayen madara komar guda goma, in dai ba iska bace ta bige su, za su iya kai shekaru 10 daram (a wuri daya).  Ni kam a kodayaushe na hada uku da uku sai in ga biyar.  Don Allah a taimaka mini da amsar.  –  Junaidu Sokoto: 09035907765
Wa alaikumus salam, Malam Junaidu.  Wannan tambaye ce mai matukar mahimmanci, wanda na san da yawa cikin mutane za su so sanin dalilan hakan, saboda samun kansu cikin irin halin da zuciyarka ta samu kanta kafin wannan tambaya.  Wannan ya sa na killace mako guda don fadada bayani.  Domin amsar wannan tambaya, in har gamsuwa ake son samu iya gwargwado, dole tana bukatar fadada bayani don komai ya fito fili filla-filla, ta hanyar fayyace bayanai sanka-sanka.
Wannan misali da ka kawo a zahirin rayuwa ta yau, don yin kiyasi a kan irin dabi’ar da duniyarmu ke gudanuwa a kai, misali ne mai kyau, amma wanda zai saukake wa mai tambaya neman dalili.  Amma idan ta bangaren asali ne, babu alaka ko kadan tsakanin bangarorin biyu.  Kana bayani a kan yadda idan aka cakuda tsakuwa da ruwa a cikin tayar mota – kamar yadda muke cakude a cikin wannan duniya a yau –  akan samu hargitsi ne mai girman gaske, da zarar motar ta fara tafiya, sanadiyyar juyawar tayar.  Amma ga shi mu da muke cakude cikin wannan duniya, wacce ta fi girma da fadi, sai dai kuma komai a natse.  Babu hargitsi. Babu cakude irin wanda ke tayar motar da ka cike da ruwa da tsakuwa (ko tsakwarkwani, kamar yadda ka kira su).  Mene ne dalili?  Dunkulalliyar amsar dai kwaya daya ce:  ka’idojin da wannan duniya tamu ke gudanuwa a kansu, sun sha bamban da wanda tayar mota ke gudanuwa a kai.  Shi yasa da ka hada uku da uku, sai ka samu biyar, maimakon shida.
Dokta Andrew Fraknoi shi ne Shugaban Sashin ilimin Sararin Samaniya a Jami’ar Foothill da ke kasar Amurka.  A cikin doguwar kasidarsa mai take: “How Fast Are You Mobing When You Are Sitting Still?” ya tattauna kan wannan batu, tattaunawa irin ta ilimi da binciken kwakwaf.  Inda yayi kokarin gamsar da masu tunani irin wannan (wanda tunani ne da galibin jama’a ke yi kan haka).  
Da farko dai ya kamata mu san wai shin, wannan duniya tamu tana juyawa ma kuwa?  In eh, to me yasa, kamar yadda ka kasa fahimta, ba a ganin alamar juyawarta a zahiri?  Sannan me yasa ba a ganin sakamakon juyarta ta hanyar samuwar hargitsi da cakuduwar abubuwa, a zahiri?  Sannan, me ye iya kadarin saurin juyawarta?  
Duniyarmu Tana Juyawa
Galibin lokuta idan ka shiga mota kana tafiya, ko jirgin kasa, da zarar ka kalli bishiyoyi ko gidajen da ke gefen hanya, sai ka ga kamar su ne suke tafiya da baya da baya, ba wai motar da kake tafiya a cikinta ba.  Har wasu kabilun Najeriya kan yi wa wasu kabilun raha, cewa wani ya shiga mota ana cikin tafiya sai ya ga kamar bishiyoyi ne kawai suke tafiya, amma motar a wuri daya take.  Sai nan take ya ce a sauke shi a ba shi kudinsa, zai je ya hau bishiya, wacce kyauata ce, tunda su ne ke tafiya.  Wannan dabi’a ce ta kiyasi da dan adam ke da ita a kwakwalwarsa.  A duk sadda ka kalli Wata da Taurari cikin dare, sai ka ga kamar wannan duniyar a tsaye take, su ne ke juyawa.  Idan ka kalli Rana ma haka za ka gani.  A idonmu take bullowa a duk safiya, sannan a idonmu take faduwa a duk yammaci.  Ga alama, a tunani takaitacce, sai a ga kamar ita ce kadai ke juyawa, mu a tsaye muke cak.  Haka lamarin yake idan kana zaune a kan kujera kana hutawa, idan wani ya ce maka a hakan ma duniyar na juyawa, sai abin ya yi maka wani bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya.  Amma a hakikanin gaskiya duniyarmu tana juyawa a duk yini.
Malaman ilimin Sararin samaniya suka ce duniyarmu na juyawa sau daya daga turkenta (“Adis”), a duk cikin sa’o’i 24.  Haka kayayyakin da ke cikinta, suna juyawa ne tare da ita duniyar baki daya.  Sannan wannan juyawa na samuwa ne cikin saurin ko tazarar mil 1000 a duk sa’a guda.  Wannan ya yi daidai da tazarar tafiyar kilomita 1600.  Wannan tazarar da saurin tafiya kan ragu idan ta doshi Arewacin duniya, a duk juyawarta.  Wannan juyi ko zagayen yini ke nan da duniyarmu ke yi, daga turkenta, wato “Adis.”
A daya bangaren kuma, akwai juyin shekara-shekara da duniya ke.  Wannan juyi na shekara na samuwa ne ta la’akari da tazarar lokaci da saurin tafiyar da duniyarmu ke yi kafin zagaye rana.  Duniyarmu kan dauki tsawon kwanaki 365 kafin ta gama zagaye Rana sau daya, wato shekara guda ke nan.  To me ya sa?  Hakan ya faru ne saboda nisan tazarar tafiya da ke tsakanin duniyarmu, da Ranar da ke hasko mu  a duk yini.  Malamai sun kiyasta cewa akwai tazarar tafiyar mil miliyan 93 (daidai da kilomita miliyan 150) tsakanin duniyarmu da Rana.  Bayan haka, titin da duniyarmu ke bi a yayin zagaye Rana cikin kwanakin shekara, da aka kiyasta nisansa, ta la’akari da nisan da ke tsakanin duniyarmu da ita kanta Ranar, bincike ya tabbatar da tazarar nisan mil miliyan 600 (daidai da kilomita miliyan 970) kafin gama zagaye guda cikin shekara.  Wannan, a cewar masana, na nuna cewa a duk cikin sa’a guda, duniyarmu na tafiya a saurin da ya kai mil 66,000 (daidai da kilomita 107,000).  Tafiya a wannan tazara da sauri, a cewar masana, na iya kai matafiyi daga birnin San Franciso zuwa babban birnin Washington DC (a duk a kasar Amurka), cikin minti uku, rak.  Wannan a tafiyar mota ana kaiwa ne cikin sa’o’i biyar; kamar daga Abuja zuwa Birnin Kano, ko daga Abuja zuwa Bauchi.
Bayan juyi da zagayen da duniyarmu ke yi, kafin mu kai ga bayanin dalilan da ke sa ba a iya gane tafiyar, da dalilan da ke sa har wa yau ba a samun hargitsi a wannan duniya tamu, zai dace mu kalli sauran halittun da duniyarmu ke gudanuwa a sarari daya da su, irin su Rana da Wata da Taurari; wai shin su ma suna juyawa ne, ko dai a tsaye suke cak, duniyarmu ce kadai ke juyawa?