Assalamu alaikum Abban Sadik da fatan kana lafiya. Filinka yana daga cikin filin da nake fara karantawa a jaridar Aminiya. Allah Ya kara maka ilimi, Ya sa albarka a cikin al’amuranka, Ya sa Sadik ya fi ka hazaka wajen irin wannan aikin alheri. Ya kuma kara mana irinku a cikin al’umma, amin. Daga Sha’aibu Garba Gurunga.
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Shu’aibu. Ina godiya matuka da wadannan addu’o’i naka masu yawa da albarka. Ina rokon Allah Ya amsa irin wannan addu’a gare ka kai ma, Ya inganta iyalinka da rayuwarka baki daya. Na gode. Na gode. Na gode.
Asslamu alaikum Baban Sadik, ni mabiyin shafinka ne a jaridar Aminiya. Barka da warhaka da fatan kana cikin koshin lafiya. Don Allah ina da tambaya, wai idan ’Yan Dandatsa (Hackers) suka yi wa mutum kutse a shafinsa na Facebook suka canja masa sunan shafi, yaya za a yi ya mayar da sunan shafinsa na asali? Na gode. Sako daga Mansur Haliru Dandin-Mahe, Sakkwato 09066749533, [email protected] <mailto:[email protected]>.
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Mansur. Da farko dai ya danganci wani irin kutse suka yi maka? Shin sun kwace shafin ne gaba daya; ba ka iya hawa don ganin abin da ke gudana? Ko kuma a’a, sun hau shafin ne, suka canja sunanka, amma kuma ba su canja kalmar sirrin da kake amfani da ita ba wajen hawa? Ko kuma sun kwace ne, amma daga baya aka dawo maka da shafin bayan sun canja sunan? In har ba ka iya isa ga shafin saboda kwacewa da suka yi, to, a nan ka ga abu na farko shi ne a dawo da shafin ma tukun daga hannunsu kafin a yi zancen yadda za a ba shi kariya nan gaba. Idan kuma ba su kwace shafin ba, sai dai sun hau sun yi aika-aika a ciki, ko kuma sun kwace amma daga baya aka dawo da shafin da karfin tuwo. A nan ne za a yi zancen hanyoyin kariya daga sake aukuwar hakan nan gaba.
Da farko dai sai ka canja kalmar sirrinka, wato “Password.” Kana iya amfani da hadakar lambobi da haruffa da kuma alamomi. Kada ka yi amfani da lambar wayarka musamman wadda jama’a suka san ka da ita, ko wacce ka lika a shafinka na Facebook. Da yawa cikin mutane kan sanya kalmar sirrinsu ta zama lambar wayar da suka yi rajistar shafin da shi, wannan kuskure ne mai girma. Kwace shafi mai dauke da kalmar sirri irin wannan ba ya da wahala ko kadan. Kamar ka gina gida ne, ka sanya masa makulli mai kyau da inganci, amma sai ka je jikin kofar gidan ka rubuta cewa, ga yadda ake bude gidan nan, cikin sauki. Bayan ka canja kalmar sirrinka, sai kuma ka canja sunanka.
Dukan wadannan abubuwa za ka yi su ne a bangaren tsare-tsare, wato: “Settings.” Idan a kan wayar salula kake hawa shafin naka da zarar ka hau, sai ka je bangaren dama daga sama, za ka ga wasu alamun layuka guda uku. Idan ka matsa za a zarce da kai jerin bayanai daga sama zuwa kasa. Daga cikin bayanan za ka ga “Settings,” a nan ne za ka asalin sunan da aka sa. Sai ka latsa wajen ka canja zuwa sunan da kake so. A gefen hagun kuma za ka ga bangaren “Password,” sai ka shiga don canjawa.
Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa. Allah Ya sa a dace, amin.
Assalamu alaikum. Don Allah ni ma ina son a aiko mini da cikakken bayani a kan Tsibirin Bermuda da tekunan da ke zagaye da shi ta: [email protected] <mailto:[email protected]>. Khalid Tukur.
Wa alaikumus salam, Malam Khalid barka dai. Bayani kan wadannan wurare da ka ambata ya riga ya gabata, ba sau daya ba, ba ma sau biyu ba, a wannan shafi mai albarka. Kamar yadda na fada a baya, babu kasidar da ta shahara fiye da wacce na rubuta kan Tsibirin Bamuda. A halin yanzu na taskance wadannan kasidu a cikin shafin Intanet na musamman da na tanada. Don haka, sai a garzaya can don samun damar karanta wannan kasida. Ga adireshin da zai kai ka kai-tsaye zuwa fannin da ke dauke da kasidar ko kadisun nan: <http://www.babansadik.com/category/teku>. Allah Ya sa a dace, amin.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kai da Sadik duk kuna cikin koshin lafiya, amin. Tambayata ita ce; don Allah yaya ake dauko bidiyo a bangaren Utube; domin na yi kokarin daukowa amma na kasa. Allah Ya kara basira, fahimta da ilimi, amin.
Wa alaikumus salam, barka dai. Da fatan ana lafiya. Yadda ake dauke sakon bidiyo daga Youtube zuwa kan wayar salula, a farko abu ne mai wahala, ko in ce ba ya yiwuwa. Amma da tafiya ta yi nisa sai aka samu manhaja ta musamman, wacce ke ba ka damar saukar da duk bidiyon da kake bukata daga shafin Youtube zuwa kan wayarka, ka iya kallo ko sauraro a duk sa’ar da ka ga dama, ko da kuwa babu Intanet a wayarka, wato: “Offline” ke nan.
Kamfanoni ko mutane da dama sun gina manhajojin wayar salula da dama da ke taimakawa wajen yin haka. Amma wanda nake amfani da ita cikin sauki, ita ce wadda kamfanin Google, mamallakin shafin Youtube, ya gina da kansa, don bai wa masu kallo damar saukar da bidiyon da ya burge su. Wannan manhaja na iya amfani da bidiyon da ke shafin cikin yanayi mai sauki, kuma ko da ba ka da “data” mai yawa, hakan ba zai zama matsala ba. Bayan duk wannan, kana iya aika wa wani ma bidiyon da ka taskance a wayarka, kai-tsaye. Idan kana bukata ka je cibiyar “Play Store” ka nemi wannan manhaja mai suna: “Youtube Go.” Allah Ya sa a dace, amin.
(Za mu ci gaba mako mai zuwa)