Shugaban Hukumar Tsaro ta Amotekun a Jihar Oyo, Janar Kunle Togun (mai ritaya), ya ce akwai yiwuwar su yi amfani da kudan-zuma da macizai masu dafi domin yaki da ’yan ta’adda a jihar.
Ya ce lokaci ya yi da za su rika yin amfani da namun daji wajen yaki da ’yan ta’adda maimakon manyan makaman zamani.
- ’Yan Hisbah sun kama mace da namiji suna lalata a tashar mota a Zamfara
- Ballon d’Or: Ko Benzema zai lashe kambun bana?
Janar Togun ya fadi haka ne a wajen taron da kungiyar Oke-Ogun Debelopment Consultatibe Forum (ODCF), ta shirya a garin Otu a karamar Hukumar Itesiwaju a Jihar Oyo.
Ya ce, ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya daban-daban ya gane wa idanunsa yadda mafarauta suke amfani da namun daji wajen yakar ayyukan ta’ddanci.
Ya nuna mamakin kan yadda mahukunta a Najeriya a lokacin yaki da cutar Kwarona suka kyale wasu ’yan ta’adda suka dinga shigowa cikin kasa daga wasu makwabtan kasashe a inda suka rika yin ayyukan ta’ddanci babu kakkautawa.
“Jihar Oyo ce kan gaba da irin wadannan ’yan ta’adda da suka shigo saboda samun kungurmin daji cikin makeken fili a yankin Oke-Ogun da ke iyaka da kasar Benin da suna buya,” inji shi.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kyale jami’an hukumar Amotekun su yi amfani da bindiga kirar AK-47 da sauran manyan makamai don gudanar da ayyukan tsaron kasa a yankin Kudu maso Yamma.
Ya ce matsalar tsaro a fadin Najeriya na ci gaba da zama babbar barazana, lamarin da ya sa dimbin mutane rasa rayukansu da dukiyoyi a sassan kasar nan.