A shekaranjiya Laraba ne kwamitin da ke da alhakin zakulo kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na Hukumar NFF ya bayar da sanarwar nada Amodu Shu’aibu a matsayin kocin kungiyar na wucin-gadi.
Kwamitin ya ce Amodu Shu’aibu tare da wadansu mutum hudu za su jagoranci kungiyar Super Eagles ne har zuwa lokacin da za a zabi kocin kungiyar na dindindin.
Sauran matimakan kocin da aka zaba don su yi aiki da Amodu Shu’aibu sun hada da Salisu Ibrahim da Alloy Agu da Imana Amakapabo da kuma Kennedy Boboye.
Tsohon kocin Eagles na riko Samson Siasia da Emmanuel Amunike yanzu sun koma matsayinsu na da. Yayin da Siasiya ya cigaba da horar da kungiyar Flying Eagles da ake fi sani da Dream Team bI wacce za ta fafata a gasar wasannin Olamfik da za a yi a Brazil a watan Yunin wannan shekara shi kuwa Amunike an koma da shi ne don ya cigaba da horar da kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 watau U-20. Samson Siasia da Emmanuel Amunike ne aka zaba a matsayin kocin Super Eagles da Mataimaki bayan tsohon kocin kungiyar Mista Sunday Oliseh ya ajiye mukaminsa.
Kwamitin ya kara da cewa daga cikin kococin da za su taimaki Shu’aibu Amodu, wajen gudanar da aikinsa akwai kocin Enugu Rangers da kuma Kocin Abia Warriors. Kwamitin ya ce ya yi haka ne don ya ba ’yan kasa damar da ta dace wajen samun gogewa a sha’anin horarwa.
Ana sa ran koci Amodu Shu’aibu zai jagoranci kungiyar Super Eagles wajen yin wasannin sada zumunta guda biyu a watan gobe da kasar Mali da kuma ta Ludemborg.
A ranar Juma’a 27 ga watan Mayun gobe ne ake sa ran Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Mali a filin wasa na Stade Robert Diochon da ke yankin Routen na Faransa sannan bayan kwanaki kadan ta sake haduwa da Ludemborg.
Kawo yanzu Najeriya tana matsayi na 63 a duniya ne a jerin kasashen da suka fi nuna kwazo a fagen kwallo a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar a watan nan, don haka akwai bukatar ta zage damtse muddin tana son farfadowa a fagen kwallo.
Idan za a tuna Super Eages ta kasa hayewa gasar cin kofin Afirka a karo na biyu a jere a watan jiya bayan Masar ta yi mata kancal. Hakan ta sa wasu suka rika yin kiraye-kirayen a dauko sabon kocin kungiyar daga waje amma Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya kekasa kasa ya ce hakan ba za ta yiwu ba, inda ya kafa kwamitin da zai bayar da shawara a kan ko ya dace a dauko sabon koci daga waje ko a’a. Daga nan ne kwamitin ya bayar da shawarar a dauki Amodu Shu’aibu a matsayin kocin kungiyar na wucin-gadi kafin a duba yiwuwar dauko sabon koci daga waje.
Amodu Shu’aibu dai ya taba horar da kungiyar Super Eagles a lokuta daban-daban a baya, amma a wancan lokaci sun yi baran-baran da Hukumar NFF ne bayan ta kore shi saboda rashin tabuka abin kirki.
Amodu Shu’aibu ya sake zama kocin Super Eagles
A shekaranjiya Laraba ne kwamitin da ke da alhakin zakulo kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na Hukumar NFF ya bayar da sanarwar nada…