✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amodu Shu’aibu ya nemi Keshi ya yi murabus

daya daga cikin Darakta a Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Amodu Shu’aibu ya shawarci Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Stephen Keshi da ya…

daya daga cikin Darakta a Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Amodu Shu’aibu ya shawarci Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Stephen Keshi da ya yi wa kansa adalci ya ajiye aiki a matsayin wanda ya kasa tabuka-abin-a-zo-a-gani a harkar kwallo a kakar wasa ta bana.

Tsohon kocin Super Eagles Amodu ya ce neman da Keshi yake yi na a sabunta kwantaraginsa a kungiyar duk da abin kunyar da ya yi na kasa hayewa da kasar nan gasar cin kofin Afirka da zai gudana a watan gobe a Ekuitorial Guinea, sam bai dace ba.
Amodu Shu’aibu wanda kwanan nan aka nada a matsayin Darakta mai bayar da shawara a harkar kwallo a Hukumar NFF ya ce tunanin da Keshi yake yi na a sabunta masa kwantaragi a Super Eagles ba abu ne mai yiwuwa ba idan kuma aka kuskura aka sabunta kwantaragin nasa to ko shakka babu ba zai haifarwa kasar nan da mai ido a harkar kwallo ba.
“Keshi ya yanke wa kansa hukunci ko ya cancanci a sabunta masa kwantaragi ko bai cancanta ba. Kamar abin nan ne da ake cewa idan ka yi mai kyau ka sani, idan ka yi mara kyau shi ma ka sani”, inji Amodu.