✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminiya za ta kawo sakamakon zabe kai-tsaye daga INEC

Da zarar INEC ta fara tattara sakamakon daga sassan Najeriya, za ku iya gani ta shafin namu

Aminiya ta bude shafi na musamman da zai rika nuna sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 kai-tsaye, domin tabbatar da cewa ba a bar masu bibiyar mu a baya ba kan wainar da ake toyawa a ko’ina kuma a kan lokaci.

Shafin namu zai rika kawo muku sakamakon zaben ne nan take daga cibiyar tattara sakamakon zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Da zarar INEC ta fara tattara sakamakon daga sassan Najeriya, za ku iya gani ta shafin namu idan kuka latsa nan, ko saman babban shafinmu.

A cikin shafin namu na musamman, za ku iya ganin yawan kuri’un da kowane dan takara ya samu a kowace jiha da kuma jimillar kuri’unsa.

Don haka ku kasance da mu.