Sanata Yunus Abiodun Akintunde mai wakiltar Oyo ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya ce wata ganawa da ya yi da ɗaya daga cikin Attajiran Arewa Alhaji Auwalu Abdullahi Rano da ake kira (A.A.Rano), a lokacin da suka je Umarah a ƙasar Saudiyya a bana, ta yi tasiri a fannin haɗa kai da ci gaban ƙasa.
Ya ce a wajen ganawar ce A.A. Rano ya nuna farin ciki da jin daɗi a kan labarin da Jaridar Aminiya ta buga kwanan baya dangane da naɗa Bahaushe da Sanatan ya yi a matsayin Mai ba shi shawara a mazaɓarsa a Jihar Oyo.
- Yadda gidajen rediyo ke yawaita a Kano
- ‘Yaron da ya sayar da ƙodarsa ya sayi wayar hannu ta N290,000’
Mutumin da Sanata Yunus Akintunde ya naɗa a matsayin Mai ba shi shawara kan harkokin ciki da waje,Alhaji Adam Haruna Yaro shi ne ya yi wannan bayani a hira da Aminiya a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
Ya ce “Bayan dawowar Sanata Yunus Akintunde daga Umarah ya gayyaci mu masu ba shi shawara duka zuwa wajen wani taro inda ya nuna matuƙar farin cikinsa game da ganawar da suka yi da attajirin na Arewa a Makka da bayanan da suka fito daga bakin A.A. Rano a kan labarin da ya karanta a cikin Jaridar Aminiya kan batun naɗa Bahaushe a wannan muƙami.
“Sanatan ya yi mana bayanin cewa irin wannan salon buga labarai a Jaridar Aminiya zai taimaka ƙwarai da gaske wajen haɗa kan al’ummomin ƙasar nan da ci gabansu.”
Alhaji Haruna Yaro ya ce Sanata Akintunde wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Yanayi kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Harkokin ’Yan sanda a Majalisar Dattawa, ya nuna mamakin jin irin waɗannan manyan mutane da ake alfahari da su a Nijeriya suna karanta Jaridar Aminiya da ake bugawa a cikin harshen Hausa.
Ya ce wannan zai taimaka wajen bunƙasa harshen Hausa a gida Nijeriya da sauran ƙasashen duniya.
Da yake amsa wata tambaya Alhaji Adam Haruna Yaro wanda shi ne Sakataren Fadar Sarkin Sasa kuma tsohon Kansilan Sasa, ya ce “Tabbas hakan ya ƙarfafa min gwiwa wajen yin amfani da wannan dama domin bayar da shawara ga Sanata Akintunde a kan buƙatun ’yan Arewa.
Musamman a fannin samun tallafin karatun ’ya’yansu a manyan makarantu da koya wa matasa ayyukan yi tare da samar da jarin ga ’yan kasuwa domin bunƙasa harkokin kasuwanci a wannan mazaɓa da Jihar Oyo baki ɗaya.
Ya nemi jama’a su lura da irin ’yan takarar muƙamai da suka kamata su zaɓa idan lokacin zaɓe ya zo.
Ya ce “Tun yanzu ya kamata jama’a su fara tantance irin waɗannan ’yan Takara a unguwanni da mazaɓu don guje wa zaɓen waɗanda babu niyyar taimakon jama’a a zukatansu sai burin cika aljihunsu.”