✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminanshi sun kashe shi kan bashin da yake bin su

Barci kawai ke raba su da abokinsu da suka kashe kan bashin da yake bin su.

Wadansu aminai biyu sun shiga hannu bisa zargin yi wa abokinsu kisan gilla saboda ya nemi su biya shi bashin kudin da yake bin su.

A Unguwar Magajiya da ke cikin birnin Zariya ne aka kashe marigayin mai suna Idris Bashir mai shekara 27, kuma dalibi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya.

Mahaifin marigayin, Malam Bashir Musa, ya ce mamacin kuma dan kasuwa ne, “To harkar kasuwancin da yake yi tare da aminan nasa ne ya sa suka ci amanarsa, suka yi masa kisan gilla saboda kudin da ke tsakaninsu.

“Su wadanda suka kashe dan nawa, idan yana gari barci ne kawai ke raba su, kuma idan ba ya nan su ne suke tafiyar masa da harkar kasuwancinsa,” inji shi.

Da yake bayyana takaicin kisan gilla da aka yi wa dan nasa saboda ya bi kadun hakkinsa, mahaifin ya nemi hukuma da ta bi masa hakkin kisan da aka yi wa dansa, saboda shi ba zai  kyale batun ba.

Aminiya ta ziyarci unguwar inda ta tarar da al’umma suna ta tururuwa domin jajantawa ga iyalan marigayin.

Bincike ya nuna cewa marigayi Idris ya rasa ransa ne a dalilin neman kudinsa Naira dubu 400 a hannun abokan nasa.

Bayanai sun ce aminan nasa su biyu sun kira shi ne zuwa kangon gidan wan dayansu a unguwar, suka kashe shi, suka jefa gawarsa a cikin wata tsohuwar rijiya, kana suka rufe ta da tifar yashi.

Rudunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin; Kakakinta, ASP Mohammed Jalige, ya gabatar da wadanda ake zargin sannan ya ce ana ci gaba da bincike.