✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amina Mohammed ta sake zama Mataimakiyar Sakatare Janar na MDD

Wa’adi na biyun dai zai fara ne daga ranar daya ga watan Janairun 2022.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, a ranar Juma’ah ya sake nada ’yar asalin Najeriya, Amina Mohammed, a matsayin Mataimakiyarsa a karo na biyu.

Mista Guterres, ya sanar da nadin ne jim kadan bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta sake nada shi Sakatare Janar a wa’adi na biyu.

Wa’adi na biyun dai zai fara ne daga ranar daya ga watan Janairun 2022, inda zai ci gaba da rike mukamin har tsawon shekara biyar. 

Ya gaji Ban Ki-moon ne a watan Janairun 2017 a zaman Sakatare Janar na MDD na tara.

Da yake zantawa da ’yan jarida bayan sanar da sake nadin nasa, Mista Guterres ya ce yana yi wa Amina Mohammed din tayin ci gaba da rike mukamin mataimakiyarsa.

“Bayan an sake min nadin mukamin Sakatare Janar, ina sake gayyatar Mataimakiyata da ta ci gaba da rike mukamin a karo na biyu, ina fatan za ta karba,” a cewar Guterres.

Amina Mohammed, wacce take tsaye a bayan Guterres a lokacin, ta yi na’am inda ta bayyana tayin a matsayin wata babbar karramawa.

Amina dai ta taba zama mai bayar da shawara ta musamman ga tsohon Sakatare Janar, Ban Ki-moon kan Cimma Muradun Karni na shekarar 2015, wanda a yanzu aka sake fasalta zuwa Cimma Muradu Masu Dorewa zuwa shekarar 2030.

Gogaggiyar jami’ar diflomasiyya, Amina wacce kuma ’yar siyasa ce ta taba rike zama Ministar Muhalli a wa’adi na farko na gwamnatin Buhari.

Haifaffiyar garin Liverpool na Burtaniya, mahaifin Amina Mohammed Bafulatanin Jihar Gombe ne kuma likitan dabbobi, yayin da mahaifiyarta kuwa ma’aikaciyar jinya ce ’yar kasar Burtaniya, kuma ita ce babba a cikin ’ya’ya mata biyar a wajen iyayen nata.

Ta yi makarantar firamare a Kaduna da Maiduguri, da kuma makarantar Buchan da ke Tsibirin Man, Sannna ta ci gaba a Kwalejin Koyar da Harkokin Shugabanci ta Henley a 1989.

Bayan kammala karatunta, mahaifin Amina ya bukaci ta dawo Gida Najeriya.