✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin Ruwa Ga Lafiyar dan Adam

Ko wace illa rashin shan ruwa a kai-a kai kan yi wa jiki kuma wane amfani dan Adam ke samu idan ya sha ruwa yadda…

Ko wace illa rashin shan ruwa a kai-a kai kan yi wa jiki kuma wane amfani dan Adam ke samu idan ya sha ruwa yadda ya kamata?
Daga Mukhtar Gafai, Katsina

Amsa: Ai ya kamata zuwa yanzu Malam Mukhtar ka san cewa idan babu ruwa babu rayuwa kuma jiki ma ba zai bar mutum haka nan ba, ba tare da ya nemi ruwa ba. Akwai hanyoyin da jiki ke nan kan bi wajen tabbatar da cewa akwai isasshen ruwa a jikin mutum. Ban da ji kishin ruwa da bushewar makoggaro da ciwon kai, idan an shiga rana, jiki kan sa koda ta rike ruwanta kada ta aika shi mafitsara in dai akwai alamun ruwan bai isa ba a jiki.
Da yake idan aka yi la’akari da cewa kusan kashi 60% na jikin dan Adam ruwa ne, za ka ga cewa ke nan a ko’ina a jikinmu akwai ruwa. Kuma da yake a daya hannun shi ma kusan wani abin mamakin, kashi 60% na kowane abinci da muke ci (wanda ba abin sha ba), shi ma ruwa ne, ka ga ke nan ko mutum ya yini bai sha ruwa ba sai dai abinci kawai, to jiki zai samu ruwan aiki a wannan rana.
Sai dai kawai kamar yadda ka fada, jiki zai fi jin dadin aiki da kuma amfana da ruwan sosai idan aka samar masa ruwa a kai-a kai, ta hanyar shan ruwa da sauran kayan shaye-shaye, ba a bar shi ya yi maleji da na abinci ba. Domin bincike ya nuna yawan shan ruwa a kai-a kai kan kiyaye matsalar kiba ko kuma ma yakan rage kibar. Sa’annan masu yawan shan ruwa sun fi marasa sha kyau da shekin fata, maza ne su ko mata. Sa’annan masu yawan shan ruwa ba su cika samun taurin bayan gida ba. Kai ita kanta kodar mai tace ruwan jiki, ta fi lafiya idan ana yawan shan ruwan.

Ni na kasance idan na yi fitsari tun karfe 10 na safe ba na sake yi sai wajen karfe shida na yamma. Ko hakan matsala ce?
Daga Usman, Kano

Amsa: Babu wata ka’ida wadda ke nuni da cewa sai bayan lokaci kaza mutum ya kamata a ce ya yi fitsari. Ya danganta da yawan shan ruwa ko kayan shaye-shaye. Abin da dai ake so mutum ya fitsarar a rana guda na ruwan jiki gaba daya shi ne kwatankwacin lita 1 zuwa 2, in dai mutum na shan ruwa yadda ya kamata kuma kodarsa na aiki sosai. Yawanci wannan lita 1 a lokacin zafi ke nan, lita 2 kuma kamar a lokutan sanyi amma akwai lokutan da mutum zai ga fitsarinsa ya karu musamman idan an sha kayan shaye-shaye da yawa a lokutan sanyi. Wato ba mamaki a irin wannan yanayi a yi fitsari kwatankwacin lita 3 ma a rana.
Idan mutum ya kiyasta ya ga a rana fitsarinsa bai kai lita 1 ba, ko yakan fi lita 3, to yana da kyau ya je a yi masa aune-aunen lafiyar jiki kamar ta suga da koda da sinadaranta ko kuma a gwada a gani ko kwayoyin cuta sun shiga suna wasa a cikin koda da mafitsara, wanda duk wadannan za su iya sa yawan fitsari canzawa a yini ko dare.

Ko me ke kawo ciwon ido da mura a lokaci guda kuma shin mene ne rigakafi?
Daga Mainasara, Funtuwa

Amsa: Yawanci kwayoyin cuta na birus ne ke sa mura da ciwon ido mai kwantsa a lokaci guda. Su kuma wadannan kwayoyin cuta da yake ba su da magani, sai dai a yi rigakafin kamuwa da su ke nan, kamar yadda ka ce. Rigakafin kamuwa daga kwayoyin cuta irin wannan bai wuce na yawan shan kayan marmari ba, wadanda suke da sindarai na bitaman da ma’adinai masu sa kaifin garkuwar jiki. Sai kuma yin nesa-nesa da wadanda aka ga suna fama da matsalar har sai sun warke.

Ni kuma idan na shaki turare mura yake sa mini. Wannan me ke kawo shi kuma mece ce mafita?
Daga Muhammad, Jahun

Amsa: Akwai wasu mutane kalilan irinka da rumfar hancinsu ba ta karbar kamshin ko warin wasu abubuwa irinsu turare a matsayin abu maras illa, sai dai a matsayin abu mai illa. Wato kusan borin jini ne na hanci, wanda ake cewa allergy a likitance. Kuma maganin shi ne mutum ya guji duk wani abu da wani bangare na jikinsa ba ya so.
Meke kawo ciwon da yake sa fuska tana kuraje manya-manya, wasu kuma su feso? Canjin ruwa ne ko na abinci ko na yanayi kuma mec cee mafita in mutum na da shi?
Daga Mudassir Maishayi Ningi da Zayyanu Tsafe

Amsa: Akwai nau’in kurajen fuska iri-iri, wadanda wasu ma idan aka ce manya-manya, to sun ma tashi daga kuraje sun zama kari. A kananan akwai wadanda kwayoyin cuta kan jawo, kamar taya-ni-muni, wasu kuma yanayi ne, kamar na zafi, wasu canjin ruwa, wasu kuma kamar na karin yawan aski ko gurzar wurin da wani abu ke kawo su.
Mafita, idan mutum na fama da kurajen fuska ko wani kari, ya je a duba shi. Likitoci da dama da sun ga irin kurjin ko karin sun san na mene ne, su rubuta magani. Sai dai akwai wadanda ko an yi amfani da maganin sun tafi za su iya dawowa idan dai abin da ya kawo su bai tafi ba.

Wai me ya sa ne idan aka yi wa mutum allura akan ce ya mulmula ko ya rika danna wurin?
Daga Maryam Garabasa, Kazaure

Amsa: To, kusan dai ba kowace allura ce idan an yi wa mutum akan so ya mulmula ba, akwai wadanda akan so a yi hakan akwai wadanda ba a so. Don haka ya kamata a tambayi wanda ya yi allurar ko ya kamata a murza wurin ko a’a. Misali, murza wurin allurar insulin kan sa allurar saurin bin jini, wanda ba haka ake so ba, murza wurin allurar warfarin zai iya sa taruwar jini a wurin, da dai sauransu. Hikimar murzawar shi ne, rage zogi da zafi da kumburi da tsami bayan wurin ya kwana.

Shin wanda ya taba samun matsalar mutuwar barin jiki ta paralysissai kamar bayan shekaru nawa yake dawowa daidai?
Daga danladi Abdulmumin, Maigatari

Amsa: Akwai wadanda sukan warke sarai daga matsalar bugun jini a kwakwalwa bayan dan lokaci (kamar bayan wata daya zuwa shekaru), akwai kuma wadanda suke samun sauki, (wasu abubuwan su dawo, wasu su zauna haka), sa’annan kuma akwai wadanda kwata-kwata ba sa warkewa. Duk wannan ya ta’allaka ne a kan bangaren da kwakwalwa ta samu matsala da yanayin mutumin, mai bin shawarwari ne ko a’a, sai kuma irin kulawa ta musamman da aka samu, tun da wasu kasashen sun fi wasu ci gaba ta hanyar kula da irin wannan ciwo na mutuwar barin jiki.