✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin keke ga lafiyarmu

A yau kowa ya san mota ko babur ake hawa a tafi wurin aiki ko wurin sana’a, ko makaranta, ga mai shi da ma wanda…

A yau kowa ya san mota ko babur ake hawa a tafi wurin aiki ko wurin sana’a, ko makaranta, ga mai shi da ma wanda bai da shi. A zamanin da, babu mota ko kuma wata na’urar motsi. Kowa ya san sayyada ake takawa ko a hau dabba (doki, alfadari, jaki, ko sa ko rakumi) a tafi kasuwa, gona ko wata harkar. To shi ma hawan dabbar wani motsa jiki ne na musamman. Wannan ce ta sa mutane da dama a wancan lokaci ba su san mene ne ciwon kiba ba, ballantana hawan jini, da suga da sauran ire-iren matsalolin da aka fi sani da cutukan zamani.
Hakika kere-kere na kimiyya da fasaha sun taimaka mana wajen saukaka ayyukan wahala da dama, amma a wani gefen kuma sun kawo wa kiwon lafiyarmu cikas. To me zai hana mu saisaita wannan dadin domin mu samu cikakkiyar lafiyar da muke nema?
Sau da yawa idan aka ba mutanenmu shawarwari na barin kaza da kaza da yin wasu abubuwa a bangaren kiwon lafiyarsu, idan sun bar wurin ma’aikacin lafiya, mun san me suke fada a bayan fage. Yawancinsu sukan ce a rabu da shawarwarin da mukan bayar din, domin su wai ‘da wahala ta kashe su, gara dadi ya kashe su’. To da mutuwa lokaci daya ake yi, idan an samu wadannan cutukan da da sauki. Inda gizo ke saka shi ne, wadannan cutuka sai sun ba mutum wahala tukun ta kowace fuska, kafin su kai shi kasa.
kididdigar baya-bayan nan ce a wannan shekara a kasashen Turai, wadanda suka kirkiro yawancin na’urorin da muka sani (kuma wadanda kowa ya san sun fi mu dabarun cimma moriyar rayuwar duniya), ta nuna cewa yawan saye da hawa keke a yanzu ya zarta na yadda ake sayen motoci ko babura, a wadannan kasashe. Wato dai tuni su wadannan Turawa, sun gano amfanin dawowa da zirga-zirga a kan kekuna. kididdigar ta nuna cewa mutane da dama suna safara zuwa wuraren ayyukansu a kan kekuna, saboda wuraren ba su da nisan da za a sha wahala, amma suna da nisan da za a ce mutum ya motsa jiki. Sauran abubuwan rayuwa kamar sayayyar gida da yawo da iyali, sai su yi a motocinsu.
Wannan dabara da suka bullo da ita tana da matukar fa’ida a bangaren motsa jiki. Da yake ba kowa ne zai iya motsa jiki yadda ake cewa a kalla na mintuna arba’in a rana, a ranakun mako biyar ko shida, idan mutum ya maida keke abin hawansa zuwa wurin sana’arsa kawai, shi ke nan ya cika wancan sharadi na motsa jiki, kuma ya yi maganin kiuya, kuma ya rage wa kansa hadarin kamuwa da hawan jini, kiba, suga, ciwon damuwa, sanyin kashi, da sauransu.
Tuka keke na ’yan wasu mintuna a ranakun mako ko ranaku biyar yana da fa’idoji da dama. Ga kadan daga cikin wadanda na zakulo:
1.    Kiyaye ciwon zuciya: kungiyar likitoci ta Birtaniya wato British Medical Association ta gudanar da wani bincike a kan wasu ma’aikata su 10,000, rabi aka ba,su keke, rabi suka rika hawa mota zuwa aiki na wani tsawon lokaci. Sakamakon ya nuna wadanda suka samu cutukan zuciya a masu hawa mota sun nunka na keke ribi biyu.
2.    Mutum zai dawo saurayi: Masu binciken lafiya a Jami’ar Stanford ta Amurka sun tabbatar cewa masu hawa keke na nishadi, ba na wahala ba, ba sa saurin tsufa. Wannan ana iya samu a kowane irin motsa jiki, amma na hawa keke ya fi.
3.    Barci mai dadi: Samun barci mai dadi ga ma’aikatan ofis yakan yi karanci. Idan ma’aikaci yana hawa keke a kullum, ba shi ba juye-juye.
4.    karfin Cinya da kugu: Inda keke ya fi sauran hanyoyin motsa jiki ke nan. Da yake aikin tukin ya fi yawa a cinya da kugu, duk namomin wannan bangare za su yi karfi, su rage kasala.
5.    Rage Tebar ciki: Tuka keke ya fi sauran hanyoyin motsa jiki sa rage tebar ciki, don aikin a wadannan wurare yake.
6.    Rage Taurin bayan gida: Tuka keke ya fi sauran hanyoyin motsa jiki motsa ’ya’yan hanji, ta yadda ba ruwan mai hawansa da yawan samun taurin bayan gida.
7.    Ga masu ciwon asma ko wani ciwon numfashi: An tabbatar cewa tuka keke ya fi guje-guje alfanu ga masu irin wannan matsala wajen bude hanyoyin numfashi.
8.    Zuwa aiki kan kari: A wasu manyan garuruwa, inda cinkoson motoci kan sa mutane bata mintuna kusan talatin a danja, mai keke ko babur ba ruwansa. Amma babur ma a wasu garuruwan yanzu ya fara zama jidali, turi ko’ina.
9.    Maganin kuiyar motsa jiki: Da dama mutane na son motsa jiki, amma saboda kiuya ba sa yi. Keke na kashe kiuya domin yana sa motsa jiki cikin nishadi, idan mutum ya maishe shi abin zuwa aiki.
10.    Rage dumamar yanayi: Duk yadda aka samu raguwar babura da motoci, ko da kaso kadan ne, to hayakin da ke bata mana muhalli ta hanyar gurbata iskar sararin samaniya, zai ragu sosai. A wasu lokuta, a manyan birane, idan akwai taron abin hawa a danja, idan ka ga hayaki kai ka ce hazo ne ya sauka.
Sai dai da yake yanzu mutane da dama sun riga sun yi kibar da wasu kekunan ma ba za su dauke su ba, yana da kyau ko irin na wuri-daya mutum ya saya a gida ya rika tukawa, saboda ya samu fa’idojin da akan samu, idan ya sabe, ya nemi na yawo. Sai dai fa’idojin wannan ba za su kai na keke mai yawo ba. Mata ma a cikin gidaje za su iya amfani da irin wannan. Wadanda ma ba sa son wannan shawara za su iya sayen na hawa a ranakun da ba aiki.
Wani abu da zai hana mu hawa keke shi ne na jin kunya, saboda a al’adarmu an saba ganinka a mota, amma a zo kuma a ganka a keke. Idan masu mota suka fara a daidaikunsu, abu ya baza gari, zai zo ya zama yayi, a manta da kunya, tunda kowa dai ya san suna da motar. Idan kuma mutum yana da ciwon zuciya, to babu shi a wannan motsa jikin, amma mai hawan jini, zai iya yi. Mai ciwon zuciya ya tuntubi likitansa domin ya san irin motsa jikin da ya kamace shi.

 

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin Tambayoyi

Likita ko mene ne riga-kafin tarin shika da na fuka ga yara?
Maman Abdullahi, Kano
Amsa: Allurar riga-kafin tarin fuka mai sun BCG, ana haifar yaro da ’yan kwanaki ake zuwa a yi masa a hannu. Ta tarin shika kuma a hade take cikin allurai uku na DPT, wacce yanzu ake kira ‘pentabalent baccin  e’ don an kara mata allurai biyu (don kare cutar mura, ciwon hanta, sarke hakora, tarin shika da ciwon ’yar wuya). Ita ana yin ta tun daga wata daya da rabi. Ana so a kalla yaro ya samu DPT ko wannan sabuwar ‘pentabalent’ har sau uku a rayuwarsa, daga yin ta farko ana maimaitawa a bayan kowane wata har sau biyu. Ga jadawalin yadda tsarin alluran yake:
Lokacin.    Allurar Riga-kafi.
Ana haifar yaro akwai allura biyu da digon-baki daya    Lambar BCG ta tarin fuka da Hepatitis B ta ciwon hanta da digon-baki na OPb ta shan-inna.
Idan ya cika wata daya, akwai allura daya da digon-baki daya    Allurar DPT ko sabuwarta ta tarin shika da sarke-hakora da ta mura da digon-baki na OPb.
A wata na biyu akwai allura daya da digon-baki daya.    A sake allurar DPT da OPb.
A wata na uku akwai allura daya da digon-baki daya.    A sake kai jariri allurar DPT da OPb.
A wata na tara akwai allura daya da digon baki daya.     Allurar kyanda da digon-bakin sinadarin bitamin A.
A wata na goma sha biyar akwai digon-baki daya.    digon-bakin sinadarin bitamin A.
Duk bayan shekaru goma.    Allurar riga-kafin sarke hakora ta Tetanus.
Duk shekara lokacin zafi.    Allurar sankarau, ga wadanda ke cikin hadarin kamuwa.

Ina da yaro dan shekaru hudu, yana da cin ruwa a kafarsa. Ko me ake yi masa ya mutu?
Ilyas, Suleja
Amsa: Cin ruwa a tsakanin ’yan yatsu masu danshi, kwayoyin cuta na ‘fungus’ ke kawo su, don haka maganin kwayar cutar ‘fungus’ ake sa masa. Inda wannan kwaya ta bambanta da sauran kwayoyin cuta shi ne, yawanci cutukan da take sawa, cutukan fata ne, kuma yawanci cutukan fata maganin shafawa ake bayarwa. Maganin shafawa ya fi maganin sha rashin hadari sosai, don haka za ka iya nema a kyamis, ba sai likita ya rubuta maka ba. Idan ka je ka ce maganin shafawa na mai kashe kwayar ‘fungus’, ko maganin cin ruwa na shafawa, don suna nan da dama. Idan aka jarraba ba su yi aiki ba, sai ka kai shi asibiti an ga wurin.
Yana da kyau dai a kiyaye yadda danshi ke shiga ’yan yatsun, domin shi ne sababi. Idan aka shafa aka warke, in danshi yana zama a kafar, dole ciwo ya dawo. Za a iya rage danshin ta hanyar yawan goge tsakanin yatsun da tawul idan ruwa ya shiga, ko a masu yawan zufa.