✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin ayaba ga fatar jiki

A ababen da muka yi magana a kansu wadanda suka shafi kwalliya, ayaba na daya daga cikin ababen da ba mu yi magana akanta ba.…

A ababen da muka yi magana a kansu wadanda suka shafi kwalliya, ayaba na daya daga cikin ababen da ba mu yi magana akanta ba. Don haka ne a yau na dauko ayaba domin a san irin sinadaren da take dauke da su, da kuma yadda za a yi amfani da ita wajen gyaran fata. Ayaba na dauke da sinadaren bitamin C kuma tana taimakawa wajen fitar da sabuwar fata a lokacin da fata taji rauni. A sha karatu lafiya.
• Ayaba na magance cizon kudin cizo a jiki. Kudin cizo na yi wa fata lahani sosai. Don haka, sai a samu ayaba a shafa a wajen da aka yi cizon.
• Idan an fadi akan keke fata ta dan kwarzane, sai a samu bawon ayaba a shafa a wajen. Ayaba na taimakawa wajen warkar da wajen, ba tare da barin wani tabo ba.
• Ayaba na taimakawa wajen sanya hakoranmu haske; bayan an wanke baki da magogi, sannan a samu bawon ayaba a goga akan hakori. Idan ana yin haka na tsawon makonni biyu za a ga cewa hakoran sun kara haske.
• bawon ayaba na warkar da irin kwarzanen da ake samu a wajen soshe- soshen fata.
• Masu yawan kurajen fuska da na jiki, sai a samu bawon ayaba a rik shafawa a fuska da jiki a kullum kafin a kwanta barci. Washe gari sai a wanke. Za a ji sauki a cikin kwanaki kadan.
•  Ko an san cewa bawon ayaba na magance ciwon kai? A samu bawon sannan a daura a inda kan ke harbawa na tsawon mintuna talatin (30) za a ji sauki.
• bawon ayaba na magance kaikayin fata. A shafa bawon a kan kurajen .
• Ayaba na taimakawa wajen haskaka takalmanmu. Ko za a gwada ne sannan a ba ni labari. Bayan an goge takalmi da tsumma sannan a dauko bawon ayaba a goga a jikin takalman za a ga takalmin ya fara sheki.