Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gargadi ’yan Najeriya kan yin amfani da mayukan shafawa masu canza launin fata domin kara kyau.
A cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, hukumar ta ce Shugabarta, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi gargadin yayin wani taron manyan jami’anta na kwana biyu da ya gudana a Legas.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Manoma Suka Ragargaji ’Yan Bindiga A Taraba
- An tsinci gawar jaririya a gefen hanya a Hadejia
Ta ce mayukan canza launin fatar wato bilicin na iya haifar da cutar kansar fata, ko su sa wasu sassan jikin mutum su daina aiki gaba daya, ko ma su kai ga rasa rai.
Farfesa Mojisola ta ce, “Ba wai kawai mun hana amfani da mayukan ba ne saboda na bilicin ne, a’a sai don saboda illar da sinadaran da ake hada su ke da shi ga lafiyar mutum, saboda za su iya haifar da cutar kansar fata ko su lalata koda da hanta.”
Ta ce ’yan kasuwa da dama na shigo da mayukan ne ta bayan fage zuwa Najeriya duk da haramcin da NAFDAC ta saka a kansu, inda ta ce yanzu bilicin ya tasam ma zama ruwan dare a tsakanin mata da ma maza.
Ta kuma nuna damuwarta kan yadda ta ce masu kwalliya da masu sarrafa mayukan ke amfani da sinadaran masu matukar hatsari ga lafiya.
Shugabar ta NAFDAC ta ce akasarin shagunan masu kwalliya da ke biranen Najeriya na amfani da kayayyaki irin su gwanda da karas da sauransu, kuma daga bisani su kunshe su domin kai wa kasuwa.
A cewarta, babban kalubalen yaki da irin wadannan kayayyakin shi ne ba a ciki kai wasu daga cikinsu kasuwa ba, an fi cinikinsu ne tsakanin mai sarrafawa da mai saye don amfani da su.
Sai dai ta yi gargadin cewa ya zama wajibi a daina wannan harkar, inda ta ce duk wanda suka kama za su gurfanar da shi a gaban kuliya don ya fuskanci doka.